Posts

Showing posts with the label Zaben Najeriya

Shugaba Buhari ya gargaɗi ƙasashen ƙetare kan zaɓen Najeriya

Image
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gargaɗi gwamnatocin ƙasashen ketare kan tsoma baki ko katsalanda a harkokin cikin gidan ƙasar musamman a lokutan zaɓe da ke tafe kasa da kwanaki 42. Majiyarmu ta rawaito cewa Shugaban ya sanar da hakan ne lokacin da yake maraba da sabbin jakadun Switzerland da Sweden da Jamhuriyar Ireland da Thailand da Senegal da Sudan ta Kudu a fadar gwamnati. Shugaban ya ce Najeriya tana aiki kafada-kafada da kungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas domin shawo kan matsalolin tsaro da bijiro da matakan tabbatar da zaɓe mai sahihanci ba tare da katsalanda ga kudin tsarin mulkin kasa ba. Ko a shekarar da ta gabata sai dai shugaba Buhari ya yi irin wannan gargadi inda yake cewa burinsa shi ne ganin anyi sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali. Abin da ya faɗawa jakadun Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta rawaito shugaba Buharin ya gargadin jakadun ketare kan su mayar da hankali kan abin da ya shafesu da dalilan turo su Najeriya, da kuma ka...

Babu abun da zai hana a gudanar da zabe a Najeriya - Gwamnati

Image
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa da al’ummar kasar cewa babu abin da zai hana gudanar da babban zaben kasar da ke tafe a watannin Fabariru da Maris din shekarar da muke ciki ta 2023 duk da barazanar tsaron da kasar ke fuskanta. Minstan yada labarai na Najeriyar, Lai Mohammed wanda ya bayyana haka a Abuja, ya ce gwamnati ba ta sauka daga kudirinta na gudanar da zabe kamar yadda aka tsara ba. Kalaman gwamnatin dai na zuwa ne bayan hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta yi kashedi cewa idan har ba a shawo kan matsalar tsaron da wasu sassan kasar ke fama da shi ba, babban zaben kasar na iya faskara. A cewar INEC ko da an iya gudanar da zaben a wasu sassan alamu na nuna cewa babu tabbacin iya gudanar da su a wasu sassa saboda matsalar ta tsaro, lamarin da tuni ya haddasa cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya. Haka zalika tuni, masana tsaro suka fara nuna yatsa ga hukumar ta INEC wadda suka ce bata da hurumin sanar da wannan mataki a radin kanta har sai ta tuntubi bangarorin...

INEC ta ce zata gurfanar da iyayen yaran da aka kama suna kada kuri'a

Image
Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC, farfesa Mahmoud Yakubu. Hukumar zaben Najeriya ta ce matukar aka samu kananan yara da ke kokarin kada kuri’a a lokacin zabuka masu zuwa, to lalle kuwa za a kama tare da gurfanar da iyayensu a gaban shari’a. Wannan dai na kunshi ne a wani sakon gargadi da hukumar zaben ta fitar, a ci gaba da daukar matakai domin hana magudi a zabukan da za a yi cikin wanna shekara. Domin sauraron cikakken rahoto kan wannan batu tare da Muhammad Kabiru Yusuf, shiga alamar sauti