Search This Blog

Sunday, 1 January 2023

Abdulmumin Jibrin Kofa ya raba tallafin naira miliyan hamsin ga al'umar Kiru da Bebeji

 


A ranar lahadi ne dan takarar majalissar tarayya a kananan hukumomin Kiru/Bebeji a jam'iyyarNNPPHon Abdulmumin Jibrin Kofa PhD,(Jarman Bebeji) ya gwanjage mutanen yankinsa da jari/tallafin kudade inda wasu suka rabauta da Dubu dari biyu(#200,000), Dubu dari daya(#100,000), Dubu Hamsin(#50,000), Dubu Ashirin(#20,000), Dubu Goma(#10,000) da kuma Dubu Biyar(#5,000).


Mutanen da suka amfana da wannan jari/tallafi sun hada da wakilan akwatuna, Exco na karamar hukuma da mazabu na Jam'iyyar NNPP da PDP na Kiru/Bebeji, KOKAS na Kiru/Bebeji, Wasu kungiyoyi masu karfi na mata da matasa a Kiru/Bebeji, Dagatan Kiru/Bebeji, Limaman Juma'a Kiru/Bebeji, Malaman Kwankwasiyya Kiru/Bebeji, Dalibai, Yan Social Media, Mafarauta, Yan Achaba, Mahauta da kuma mutane masu bukata ta musamman.

Wannan taro ya sami halartar yan takarkaru na Kiru/Bebeji, manyan jagorori tare da  shuwagabannin jam'iyyar NNPP/PDP na Kiru/Bebeji.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kano Business Community Endorses Gov. Yusuf for Second Term

The leadership of the Kano business community, comprising representatives of 25 major markets across the state, has endorsed Gov...