Skip to main content



Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi jin matsayin shari'a daga babbar kotun duniya kan mamayen da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa.

Ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƙasa 87, sai 26 suka nuna adawa da shi ciki har da Amurka da Burtaniya.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya tana da ƙarfin yanke hukunce-hukuncen da wajibi ne a yi musu biyayya, amma ba ta iya tilasta aiki da su.

Ƙuri'ar ta ranar Juma'a, ta zo ne kwana ɗaya bayan rantsar da Benjamin Netanyahu a matsayin firaminista na gwamnatin Isra'ila mafi tsaurin ra'ayi a tarihi.

Isra'ila ta mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma ko da yake ta janye daga Gaza amma har yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya tana kallon yankin a matsayin wanda ke ƙarƙashin mamaye.

Isra'ila na iƙirarin cewa gaba ɗayan Ƙudus ne babban birninta, yayin da Falasɗinawa ke cewa Gabashin Ƙudus ne babban birnin wata ƙasarsu da za a kafa nan gaba.

Amurka na cikin tsirarun ƙasashen da suka amince da Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Falasɗinawa na iƙirarin mallakar Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Ƙudus wanda Isra'ila ta haɗe cikin ƙasarta da Zirin Gaza don kafa ƙasar da suke fatan gani a nan gaba.

Jami'an Falasɗinu sun yaba wa ƙuri'ar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa a matsayin wata nasara a gare su.

Nabil Abu Rudeineh ya ce lokaci ya yi da za a kama Isra'ila "da alhaki kan laifukan da ake ci gaba da aikatawa a kan jama'armu".

Sabon firministan Isra'ila, a nasa ɓangare, ya bayyana matakin a matsayin wani "abin ƙyama"."Al'ummar Yahudawa ba 'yan mamaya ba ne a ƙasarsu ta haihuwa kuma ba masu mamaya ba ne a babban birnin Ƙudus da Allah ya ba mu kuma babu wani ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya da zai iya kankare wannan gaskiyar abin tarihi," in ji Mista Netanyahu ranar Asabar da yamma.

A ranar Alhamis ne, Benjamin Netanyahu ya sake dawowa a matsayin fira minista na wata gwamnatin gamin gambiza ta ƙawancen masu tsattsauran ra'ayin kishin ƙasa da masu tsananin kishin Yahudanci na ainihi.

Ƙa'idar farko da ke yi wa gwamnatin jagora wadda aka wallafa ranar Laraba, ta ayyana cewa "Al'ummar Yahudawa ne ke da 'yancin da ba wata tababa a kan duk yankunan ƙasar Isra'ila, su kaɗai".

Ta ce a ciki har da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamaye kuma ta yi alƙawarin "ci gaba da kuma bunƙasa" matsugunnai a can.

Yahudawa kimanin 600,000 ne ke zaune a matsugunnan da aka gina guda 140 tun bayan mamayen da Isra'ila ta yi wa Gaɓar Yamma da Gabashin Ƙudus a shekarar 1967.

Mafi rinjayen ƙasashen duniya na kallon matsugunnan a matsayin haramtattu a ƙarƙashin dokokin ƙasashen duniya, ko da yake, Isra'ila tana jayayya da hakan.

Sabuwar gwamnatin ta kuma yi alƙawarin halatta wasu cibiyoyin soji kimanin 100 a Gaɓar Yamma waɗanda aka gina ba tare da izinin Isra'ila ba - kuma za ta haɗe Gaɓar Yamman da ƙasarta.

Mai magana da yawun Burtaniya a MajaDu na cewa ba ya jin kai batun gaban kotun hukunta manyan laifuka zai "taimaka wajen dawo da ɓangarorin kan teburin tattaunawa". Ya kuma ce hakan "bai kamata ba tun da babu yardar duk ɓangarorin biyu" na neman shawarar kotu a kan "abin da tun ainihi taƙaddama ce ta ɓangare biyu".

(BBC HAUSA)





Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki