Obasanjo ya zama tamkar dan bakin ciki - Fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taɓa daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baƙin ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ƙasa ba.

Fadar shugaban ƙasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alƙawura a kanta.

Haka kuma fadar shugaban ƙasar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ƙarya domin ya samu ƙuri'unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ƙuri'unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma ce Obasanjo yana baƙin ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da'awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe fiye da wanda ya kawo sa kan karagar mulki.

Haka kuma fadar ta zargi Obasanjo da lalata dimokraɗiyya a Najeriya bayan kitsa tsige wasu gwamnoni a ƙasar da suka haɗa da Joshua Dariye da Rashidi Ladoja da Peter Obi da Chris Ngige da Ayo Fayose.

Wannan martanin na fadar shugaban Najeriya duk na zuwa ne bayan tsohon Shugaban Najeriyar Chief Olusegun Obasanjo ya ce Peter Obi ne zaɓinsa a zaɓen 2023 haka kuma Obasanjon ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki