Search This Blog

Sunday, 1 January 2023

El-Rufai ya yi wa fursunoni 11 afuwa a Kaduna



Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya amince da yin afuwa ga fursunoni 11 daga gidajen yarin jihar domin murnar sabuwar shekarar 2023.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwaman kan kafofin yaɗa labarai na gwamnan jihar Mista Muyiwa Adekeye ya fitar.

Afuwar ta shafi fursunonin da suka nuna kyakkyawan hali da waɗanda suke fama da rashin lafiya kamar yadda sanarawar ta bayyana.

Haka kuma gwamnan ya nemi al'ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu son zaman lafiya, tare da fatan cewa aikin da ya faro tun a shekarar 2015 domin inganta rayukan al'umma jihar za su ci gaba a gwamnati mai zuwa.

(BBC HAUSA)

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...