Search This Blog

Saturday, 6 May 2023

Zaben Adamawa: An Ba Da Belin Kwamishina Hudu

 


’Yan sanda sun bayar da belin Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, bayan da ya yi kwana uku a tsare a hannunsu.

’Yan sanda sun cafke shi ne kan wata sanarwa mai cike da rudani da ya yi  cewa Sanata Aisha Dahiru Binani ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, alhali ba a kammala karbar sakamakon karashen zaben ba.

Tun a lokacin INEC ta soke sanarwar, sannan ta bukaci ya gabatar da kansa a hedikwatarta da ke Abuja, amma maimakon ya je, sai ya yi layar zana.

Daga bisani hukumar ta rubuta Shugaban ’Yan Sandan Najeriya wasikar neman ya binciki kwamishinan zaben, kan yamutsa hazon da ya yi.

Amma wata wasika da ya aike wa shugaban ’yan sanda, Hudu ya ce ya yi sanarwar ne a bisa doka, saboda dalilan tsaro.

A ranar Talala ’yan sanda suka sanar cewa sun kama Hudu, wanda ya ce ba ya nadamar sanarwar da ya ya yi cewa Binani ta ci zabe.

Amma kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Juma’a cewa rundunar ta bayar da belin kwamishinan zaben.

Muyiwa ya cen an umarci Hudu ya rika zuwa hedikwatar rundunar a ranakun aiki domin ci gaba da binciken da ake gudarwa.

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...