Abun Da Ya Haddasa Yakin Sudan Jamhuriyar Musulunci (Kashi na daya) - Datti Assalafiy
Shimfida:
Akwai taba addini a yakin Sudan, saboda shi tsohon shugaban Kasar Sudan Umar Albashir wanda aka masa tawaye aka hambarar dashi da karfin tsiya ya bawa Musulunci kariya sosai a Sudan, yana bawa Musulunci kariya a Sudan wanda ko Saudiyyah bata yin irinsa a Kasarta
Yana daya daga cikin shugabannin Kasashen Musulunci a duniya wanda idan makiya Musulunci suka taba addinin Allah da Musulmai yake fitowa yayi magana, Kasar Iran daular masu bin addinin shi'ah sun taba yin mummunan batanci ga Sahabban Annabi (SAW) guda biyu Abubakar da Umar, a ranar ya kori Ambasadar Kasar Iran, kuma yasa aka rushe embassy na Iran dake Sudan, aka gina Sabon Masallaci a gurin, aka sanya wa Masallacin sunan Abubakar da Umar wato sunan Sahabban Annabi (SAW)
Lokacin Shugaba Umar Albashir babu gidan sayar da giya a Sudan, babu gidan karuwai a Sudan, babu gidan caca da sauran guraren sabon Allah, mata basa shiga harkokin shugabanci, to wannan kariyar da ya bawa Musulunci, sai Kasar Amerika ta dauki hayar wasu gurbatattun Musulmai suka tayar da zanga-zanga mai taken "HURRIYA-SALAMA-ADALA". ma'ana 'yanci, adalci da zaman lafiya, wato su sun gaji da dokokin Musulunci tsaurara suna neman 'yanci don suyi rayuwa irin na yahudu da nasara, akan haka suka kifar dashi, to Allah suka taba
A lokacin da suke dab da zasu kifar da Albashir, ya fito yayi rantsuwa yace Billahillazi zaku ce na fada muku idan kuka sake kuka hada kai da Amerika, Wallahi sai kunyi da na sanin abinda kuke min na zanga-zanga da tawaye, to bayan sun kifar dashi, shugaban Sojojin Sudan General Abdel Fattah al-Burhan da ya maye gurbinsa karen farautar Amerika da Isra'ila ne, nan take ya bude wa Kasar Isra'ila hanyar mubayi'ah, kuma kafin fara wannan yakin, a ranar 1-2-2023 General Al-Burhan ya gayyato Ministan harkokin waje na Kasar Isra'ila Eli Cohen zuwa Khartoum babban birnin Sudan, wannan ne abinda ya faranta ran Amerika ta cire manyan takunkumi da ta kakabawa Sudan lokacin mulkin Umar Albashir, kuma ta nemi Shugaban Sojojin ya mika mata Albashir don ta wulakantashi
An yaudari Mutanen Sudan da neman 'yanci, to ga inda 'yancin ya kaisu a yau, mutum sama da dubu dari uku suna sansanin 'yan gudun hijra a sati uku da aka fara wannan yakin, 'yan Sudan sama da dubu dari da hamsin sun tsere daga Kasar, an kashe mutane kusan dubu daya zuwa yanzu, asibitoci sun rufe, manyan kasuwanni sun rufe, babu inda za'a kai marassa lafiya, kafar internet na Kasar na neman rufewa gaba daya, harkokin bankuna na Kasar duk sun tsaya saboda mummunan harin bomb da akayi a babban bankin Kasar Sudan, farashin kudin Sudan yayi mummunan karyewa mafi muni a tarihi, a tsakanin sati uku da fara wannan yakin anyi barna a Sudan wanda za'a dauki tsawon lokaci kafin a gyara lamura, na karanta bayanin wani masanin tsaro yace za'a kai nan da shekaru 15 kafin Sudan ta dawo hayyacinta ko a gama wannan yakin
Wannan bayanin da nayi shinfidane kawai, ku biyoni a rubutu na gaba don jin abinda ya haddasa wannan yaki da tarihin yakin, da inda aka nufa, akwai babban darasi garemu akan wannan kazamin yaki da yake faruwa a Sudan
Muna rokon Allah Ya tausaya wa bayinSa salihai da kananan yara da mata dake Sudan Ya kawo musu mafita na alheri
Allah Ya sa fitinar ta cinye wadanda suka tayar da ita da wadanda suka tsara zanga-zangar kifar da shugaba Umar Albashir