Gamu Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 4- Dr Dukawa

HALIN DA TITUNAN NAJERIYA SUKE CIKI
Tafiyar da muka yi daga Kano zuwa Yola ta dauke mu kimanin awa tara (9.30 na safe – 6.30 na yamma). Kuma na yaba da tukin direbanmu, wani matashi mai suna Uzairu dan kimanin shekara 25/6. Wannan tafiyar ta tuna min da wani majigi da shahararren masanin kimiyar siyasa, Farfesa Ali Mazrui, ya yi a shekarun 1980. Ali Mazrui dan asalin Kenya ne, ya auri ‘yar Najeriya, sun rayu a America har rasuwarsa. 

Guda daga cikin hanyoyin da Ali Mazrui ya bi wajen nuna tazarar da take tsaknin manyan kasashe da masu tasowa shine yadda ya dauko hoton wani titi a wata babbar kasa (watakil America) da motoci suna gudu kowacce a layinta. Sai ya ce: “duk wanda ka gani yana tuki yana kwane-kwane anan, to a cikin maye yake”. Sai kuma ya dauko wani titi na wata kasar mai tasowa (watakila Kenya ko Najeriya), da motoci suna ta kwane-kwane suna kaucewa ramukan kan titi. Sai ya ce: “anan kuma, duk wanda ka gani yana tafiya sambel babu kwane-kwane to a buge yake!” 

Yau kimanin shekara arba’in da wannan majigin na Ali Mazrui amman har yau titinan Najeriya sai ana tafiya ana ta kwane-kwane a wurare da yawa. Ga arziki Allah yana ta dada tuttudowa kasar amman lafiyayyun hanyoyin mota sun gagara. Illolin rashin hanya mai kyau suna da yawa. Ko ba a yi hatsari an rasa rayuka da dukiya ba fargabar yiwar afkuwar hakan ta ishi matafiya. Ga kuma saurin lallacewar abin hawa. 

Sai dai ko babu komai na lura gwamnatocin jihohin Adamawa da Taraba sun kokarta wajen samar da titinan cikin gari da magudanan ruwa masu kyau. Amman fa akwai tarin shara da ta rufe magudanan ruwa masu yawa. Yana da matukar muhimmanci gwamnatocinmu su samo kan yadda za a yi da shara a birananmu. Sannan akwai bukatar ko hadin guiwa ne su yi wajen gyara manyan titina idan gyaran ya gagari gwamnatin tarayya.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki