Ya Kamata A Yi Wa Ruqayya Aliyu Jibia Adalci - Nasir Salisu Zango
Ruqayya Aliyu Jibia’yar jarida ce dake wakiltar gidan talabijin na Tambarin Hausa a jihar Katsina,kuma a kwanakin nan ta samu sabani da ‘yansandan jihar Katsina bayan da ta wallafa bidiyo a shafin ta na TikTok wanda a ciki ta bayyana rashin da cewar abin da ‘yansanda keyi na sakin bidiyon wadanda ake zargi da laifi musamman yadda ake nuna fuskokin su.
Amma abin takaici bayan sakin bidiyon sai Ruqayya tayi kukan cewar, ‘yansandan sun ci zarafin ta har ma an kama ta an fasa mata waya an kuma kai ta gaban sarkin Katsina wanda acan ma tace an yi tayi mata barazana. Kamar yadda ta bayyana.
Na dai tuntubi mai magana da yawun rundunar‘yansandan jihar Karsina CSP Gambo Isa wanda yace min Abin da Ruqayya take musu akan aikin su bai dace ba.
Babban abin takaicin shine a daidai lokacin da Ruqayya ke cikin firgici da barazana sai kuma muka ga gidan talabijin din da take wa aiki sun saki takardar dake cewar Ruqayya ba ma’aikaciyar su bace. Kome suke tsoro oho.
Kamar yadda kuke gani dai ga katin shaidar aiki na Ruqayya da takardar daukar ta aiki, bayan haka ma akwai shaidar biyan ta albashi da suke,kaga kenan tsakanin gidan talabijin din da Ruqayya Waye ya zukala karya?
Idan har Ruqayya tayi gaskiya to abu ne me sauki ta iya neman hakkin ta a gaban kotu.
Yanzu haka Ruqayya tace ta buya saboda firgici da take ciki,anan ina kira ga kungiyoyin kare hakkin dan adam da kungiyar CPJ me kare hakkin’yan jaridu da sauran masu fafutuka musamman lauyoyin kare hakkin marasa galihu domin kawowa Ruqayya dauki.
Shin akwai laifi a cikin bayanan da Ruqayya ta wallafa wanda har yasa ‘yansanda ke cigaba da neman ta? Yakamata a je kotu a tantance.