Labari Da Dumiduminsa: Tawagar Farko Ta Maniyyatan Kasar Pakistan Mai Dauke Da Mutum 138 Sun Sauka A Makkah

Kashi na farko na jigilar alhazan Pakistan ya isa Makkah domin kammala shirye-shiryen mahajjatan Pakistan.

Wakilin Rediyon Pakistan Javed Iqbal ya ruwaito daga Makkah cewa rukunin mutane 138 sun hada da Moavineen 19, kwararrun likitoci 67 da kuma jami’an ma’aikata 52 na ma’aikatar kula da harkokin addini.

Tawagar za ta kafa sansanonin kula da lafiya tare da kammala wasu shirye-shirye da suka hada da wurin kwana, sufuri da kuma wuraren cin abinci ga alhazan Pakistan.

Yana da kyau a ambaci cewa aikin jigilar alhazai na Pakistan zai fara aiki daga gobe.

Bayan shekarar 2019, wannan shi ne aikin Hajji na farko mai cikakken karfi wanda a karkashinsa kimanin alhazan Pakistan 180,000 ne za su tafi kasar Saudiyya don sauke farali.

A bisa umarnin na musamman na ministan harkokin addini Talha Mahmood, ma'aikatan ma'aikatar suna yin kokari sosai don ganin aikin Hajjin bana ya samu nasara.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki