Kotu ta ɗaure Ekweremadu shekara tara a gidan yari
An yanke wa wani hamshaƙin ɗan siyasar Najeriya, Ike Ekweremadu, da mai ɗakinsa, hukuncin ɗauri a gidan yari bayan kotu a Birtaniya ta same su da laifi kan yunƙurin safarar sassan jikin ɗan'adam.
Kotun ta yanke musu hukuncin ne tare da wani likita "mai shigar musu tsakani" bayan sun kai wani matashi Birtaniya daga Lagos.
Yanzu dai, Sanata Ike Ekweremadu zai shafe kusan shekara goma a gidan yarin Birtaniya.
Sanatan mai shekara 60, da mai ɗakinsa Beatrice 'yar shekara 56, sun so a cire wa matashin sashen jikinsa ne da nufin dasa wa 'yarsu Sonia 'yar shekara 25, kamar yadda ma'auratan suka bayyana wa Kotun Old Bailey
An kuma samu "mai shiga tsakani" Dr Obinna Obeta da matar sanata Ekweremadu, Beatrice, da laifi
Tun da farko kotu ta samu ma'auratan da likita Dr Obinna Obeta, mai shekara 50, da laifin haɗa baki don ci da gumin mutumin ta hanyar cire ƙodarsa.
Ita ce shari'a ta farko a ƙarƙashin dokokin haramta bautar zamani.
Yadda aka kama Sanatan Najeriya bisa zargin yunkurin cire sassan jikin mutum
24 Yuni 2022
Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam
23 Maris 2023
Matashin da aka yi yunƙurin cire wa ƙoda domin bai wa ƴar Ekweremadu
25 Maris 2023
Ike Ekweremadu, wanda alƙalin kotun ya bayyana a matsayin "jigon da ya shirya abin da ya faru gaba ɗaya", zai yi zaman gidan yari tsawon shekara tara da wata takwas.
Hkaa kuma ta yanke wa Dr Obinna Obeta hukuncin ɗaurin shekara 10 bayan alƙalin ya gano cewa shi ne ya samo mutumin da zai ba da gudunmawar wanda matashi ne talaka, kuma mai rauni.
Ita kuma matar sanatan na Najeriya, Beatrice Ekweremadu an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara huɗu da wata shida saboda yadda ta ɗan sa hannu wajen aikata laifin.
A wani zaman yanke hukunci da aka nuna ta talbijin, Mai shari'a Justice Johnson ya nunar cewa Ike Ekweremadu, mutum ne da "ƙimarsa ta yi matuƙar zubewa".
Ya ce: "Masu fasa-ƙwaurin mutane a tsakanin ƙasashen duniya don cire sassa jikin mutum, abin da suke aikatawa wani nau'in bautar da ɗan'adam ne."
Mutumin da suka yi safarar tasa, wani talaka ne mai sana'ar tireda a Lagos, da suka kai shi Birtaniya don a cire masa ƙoda guda ɗaya, da nufin dasa wa 'yar Ekweremadu.
Ya dai tsere ne saboda tsoron mutuwa, inda ya kai kansa ofishin 'yan sanda kimanin shekara ɗaya da ta wuce kuma ya ba da rahoton abin da ya faru, bayan asibitin Royal Free Hospital ya nemi a dakatar da aikin da aka tsara yi a kan kuɗi £80,000.
BBC