Hukumar NAHCON Za Ta Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Akan Kula Da Aikin Hajji

A ci gaba da shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2023, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta shirya taron bita na yini daya kan kula da aikin hajji a dakin taro na gidan alhazai a ranar Asabar.

Shirin mai Taken Bayar da Horo da Ƙarfafa nagartar aiki ga Shugabannin ƙungiyoyin a aikin Hajji" ana sa ran babban darakta kuma mai ba da shawara kan harkokin Hajji da Umrah a Saudiyya, Dr. Badr Muhammad Al solamin zai gabatar da jawabi a yayin taron. 
A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da hulda jamaa na hukumar, Mousa Ubandawaki, y ace Sauran wadanda zasu gabatar da jawabi sun hada da: Dr. Mohammed Shokri Zamzami, Babban Darakta na Kwamitin Tawwaf na Alhazai da Jamrat Grouping a Muassassah, Abdullah Hammadu Adam, Jami'in Gudanarwa, Muassassah.

Sama da Mahalarta 90 ne ake sa ran za su halarci taron, wanda ya kunshi mambobi da shuwagabannin Kungiyar shugabannin hukumomin kula da Dadin Alhazai ta Jihohi, Manyan Jami’an Gudanarwa na kamfafonin jigilar aikin haji da Umrah masu Zaman Kansu na Kasa da Kasa, Daraktoci da Ma’aikatan Gudanarwa na NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki.

Wadanda zasu gabatar da jawabin, sun iso kasar nan ne bisa samun kyakkyawar tarba daga Shugaban Hukumar NAHCON, Alh. Zikrullah Kunle Hassan, Kwamishinan hukumar mai Kula da Ma’aikata da Kudi (PPMF), Alh. Nura Hassan Yakasai, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Watsa Labarai da Ayyukan Laburare (PRSILS), Sheikh Suleman Mommoh da Kwamishinan Ayyuka, Lasisi da Yawon shakatawa (OIL), Alh. Abdullahi Magaji Hardawa, da Babban Ma'aikatan Gudanarwa na Hukumar.
 


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki