Yakin Sudan: Sojoji Da ’Yan Tawaye Za Su Koma Teburin Sulhu A Saudiyya


Sojoji da mayakan RSF da ke yakar juna a Sudan za su koma kan teburin sulhu ranar Lahadi bayan sun kwana suna ba-ta-kashi a Khartoum, babban birnin kasar.

Wani babban jami’in gwamnatin Sudan ya ce za su koma tattaunawar ne bayan barkewar yaki tsakaninsu duk da yarjejeniyar da suka sanya hannu na kare fararen hula da ayyukan jin kai.

Jami’in ya bayyana cewa kasar Saudiyya mai masaukin baki ta gayyaci Babban Hafsan Sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan zuwa babban taron kasashen Larabawa da zai gudana a birnin Jidda ranar Juma’a.

Sai dai wasu jakadun kasashen Larabawa sun bayyana cewa ba a tsammanin zuwan Janar Burhan zai halarci taron ba saboda dalilan tsaro.

An gayyaci Janar Burhan ne a matsayinsa na shugaban kwamitin rikon kasar, wanda aka dora wa alhakin tsara yadda za a mika mulki ga zababbiyar gwamnati anan gaba,

Abokin hamayyarsa kuma shugaban mayakan RSFk, Janar Mohamed Hamdan Dagalo kuma shi ne mataimakinsa a kwamitin.

Wani jakadan kasar Saudiyya ya bayyana cewa kawo yanzu dai ba a fitar da sunayen wadanda za su wakilci bangarorin a zaman ba.

Rikicin da ya barke bagatatan a watan Afrilu a Sudan ya yi ajalin kusan mutum 800, tare da tilasta wasu sama da 200,000 gudun hijira zuwa kasashe makwabta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bayan haka wasu sama da 700,000 sun yi  gudun hijira zuwa wasu sassan kasar.

A ranar Alhamis Saudiyya da Amurka suka jagoranci sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da nufin kare fararen hula da bayar da damar ci gaba da ayyukan jin kai.

Sai dai kuma bangarorin sun ci gaba da luguden wuta a sassan birnin Khartoum, cibiyar rikicin, kafin wayewar garin Asabar.

Ana dai sa rai cewa a zaman ranar Lahadi bangarorin za su tatttauna matakan aiwatar da yarjejeniyarsu ta ranar Alhamis kan yadda za a kare fararen hula da ma’aikatan agaji da kuma janye sojoji daga yankunan fararen hula.

Za kuma a tattauna yadda za a kawo karshen rikicin, wanda zai kai ga kafa sabuwar gwamnatin farar hula a Sudan.

Bisa abin da aka saba gani, babu wani daga cikin bangarorin da ke nuna alamar sassauci, inda suke ta gwabza fada, duk da cewa sun yi yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sai dai kawo yaznu, RSF ta yi alkawarin mutunta yarjeniyar ranar Alhamis, amma har yanzu bagaren sojojin kasar bai ce uffan ba.

AMINIYA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki