Kotu Ta Tsare Dokta Idris Dutsen Tanshi A Gidan Gyaran Hali

 


Wata Kotun Majistare da ke Bauchi ta ba da umurnin a tisa keyar malamin addinin musuluncin nan, Dokta Idris Abdulaziz, wanda aka fi sani da Dutsen Tanshi zuwa gidan gyaran hali bisa zargin kawo hargitsi da tayar da hankalin jama’a.

Majiyoyi da ga rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi da Hukumar Shari’ar Musulunci a Bauchi da kuma Almajiran malamin, sun tabbatar da tsare shi a gidan gyaran hali.

A kwanakin baya ne wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya, ta rubuta takardar koke ga kwamishinan ’yan sandan jihar, bisa zargin cewa Malamin ya yi batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi).

Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda suka gayyaci dukkan bangarorin da abin ya shafa kuma tun a makon jiya aka nemi malamin ya amsa goron gayyatar.

Wasu daga cikin almajiransa sun bayyana cewa, Dokta Abdulaziz wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, ya amsa gayyatar ’yan sandan a ranar Litinin kafin ma a gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan zargi.

Daliban sun bayyana cewa ’yan sanda sun gurfanar da malamin ne a Babban Kotun Majistare mai lamba ta 1 kan zargin da ake masa.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa, alkalin kotun ya hana bayar da beli, sannan ya bayar da umarnin a ajiye wanda ake kara a gidan gyaran hali, tare da bayar da umarin sake dawo da shi gaban kotu ranar Talata.

A watan da ya gabata ma malamin a cikin hudubarsa ta Azumin Ramadana, an zarge shi munana ladabi ga Manzon Allah (SAW).

Tun a wancan lokaci dai lamarin ya rika yamutsa hazo har ta kai ga wasu malaman addinin Islama sun yi masa inkari.

Sai dai kuma an wasu malaman da suka goyi bayansa da cewa kalamansa na an turba ta gaskiya.

AMINIYA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki