Dan jarida, Ndace, ya wallafa littatafai uku kan yadda Buratai yai nasarar yaƙi da Boko Haram/ISWAP

Jibrin Baba Ndace, tsohon wakilin jaridar Blueprint a ɓangaren tsaro, ya bayyana cewa ya rubuta littattafai uku ne a kan yaƙi da ta'addanci duba da yadda tsohon Shugaban Hafsoshin Sojojin Ƙasa, COAS, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), duba da irin jajircewar sa wajen yakin.

An ƙaddamar da littattafan, masu taken  “Walking the War Front with Lt. Gen. TY Buratai,” “Duty Call Under Buratai’s Command” da kuma  “The Lonely Grave and Other Poems" a ranar Asabar da ta gabata a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua da ke Abuja.

Da ya ke magana game da dalilin da ya sa ya fara aikin wallafa litattafan, wanda ya kwashe shekaru biyar yana rubutawa, Ndace, tsohon babban sakataren yada labarai, CPS, ga Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya lura cewa ya sami kwarin gwiwa da bukatar rubuta littattafan ne na yakin da ake yi da masu tada kayar baya a matsayin sa na ganau ba jiyau ba.

“Wadannan littattafan sun samu goyon baya da gudunmawa daga tsoffin sojoji da suka taka rawa a fagen yaƙi. Sojojin da su ka sadaukar da rayukansu don bauta wa ƙasar mu da jajircewar da suka nuna da kuma abubuwan da suka faru na ban tsoro.

“Daga cikin sojoji da masu yi wa kasa hidima, Laftanar Janar TY Buratai ya mamaye babban bangare na labarin.

“Lt. Janar TY Buratai Janar ne na sojan Najeriya mai ritaya, tsohon babban hafsan sojin kasa, wanda aka nada a shekarar 2015 kuma ya yi ritaya a watan Janairun 2021,” in ji mawallafin.

Da ya ke sanya albarka a wajen taron, Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ce littattafan da ke bayyana yakin da ake yi da mayakan Boko Haram/ISWAP a yankin Arewa maso Gabas an rubuta su ne musamman domin taimakawa wajen ganin irin ta’addancin da su ke yi a kan yan kasa.

Ya kara da cewa littattafan sun kuma nuna irin kwazon Sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro, Civilian JTF su ke yi wajen yaƙi da ƴan Boko Haram da ISWAP a karkashin jagorancin Hafsan Sojoji na 20, Laftanar Janar TY Buratai.

Shettima, wanda Sen. Ibrahim Hassan Hadejia ya wakilta, ya yaba wa Ndace, mawallafin littattafan wajen kwazo da hazakar da ya nuna a matsayin sa na ganau a yaki da ƴan ta'adda.

Ya bayyana littattafan na Ndace ba kawai a matsayin 'tatsuniyoyi kawai ba, sai dai cewa fitattun ayyukan basira ne na gaskiya da gaskiya.

Shettima ya lura cewa masu karatun littattafan na Ndace da aka buga a cikin su za su sami labarin gaskiya na yadda sojojin Najeriya su ka kasance a sahun gaba wajen kare martabar kasar daga kungiyar Boko Haram da kungiyar Islamic State of West Africa, ISWAP.

Sauran manyan baki da su ka tofa albarkacin bakinsu, musamman Ministan Tsaro, Manjo - Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya), sun yabawa Ndace bisa gagarumin aikin da ya yi na fito da yadda yaƙi da Boko Haram da nasarorin da aka samu.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki