Barcelona Ta Lashe La Liga Karon Farko A Shekaru Hudu

Barcelona ta lashe gasar La Liga a karon farko cikin shekaru hudu, bayan samun nasarar lallasa Espanyol da ci 4-2 a wasan da suka fafata a ranar Lahadi.

Robert Lewandowski ne ya ci wa Barcelona kwallaye biyu sai kuma na farko tun bayan zuwansu Barca da Alejandro Balde da Jules Kounde suka jefa wa kungiyar.

A yanzu Barcelona ta bai wa Real Madrid tazarar maki 14 da ke biye da ita a mataki na biyu yayin da ya rage wasanni hudu a karkare La Liga ta bana.

Barca ce kungiyar da babu kamarta a fagen tamaula a Sifaniya a bana, inda ta rika jan ragama a saman teburin La Liga tun daga wasan mako na 13.

Barcelona ta lashe La Liga jimilla 27 a tarihi, kuma wannan ita ce ta kakar wasa ta farko da tsohon dan wasan kungiyar, Xavi Hernandez ya jagorance ta a matsayin koci.


Sai dai duk da wannan bajinta da Barcelona ta yi a iya La Liga, ta gaza kai bantenta a nahiyar Turai, inda aka tankado keyarta tun daga zagayen rukuni a Gasar Zakarun Turai, sannan kuma bayan ta koma Gasar Europa, a can ma Manchester United ta yi wancakali da ita.

AMINIYA 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki