Game Da Tafiya Da Motar Haya A Najeriya Kashi Na Daya

Daga 
Dr. Saidu Ahmad Dukawa

SHIMFIDA
A ranar Talata, 25/4/2023, na shiga motar haya daga Kano zuwa Yola, babban birnin jihar Adamawa a Najeriya. Ranar Alhamis kuma, 27/4/23, na shiga wata motar hayar daga Yola zuwa Jalingo, babban birnin jihar Taraba. Rabona da tafiyar motar haya wacce ta kai tsawan haka tun a shekarun 1983 zuwa 1984 a yayin da na yi hidimar Kasa (NYSC) daga jihar Kano zuwa jihar Bauchi, sai kuma jihar Lagos da na je bayan kammala hidimar kasa a wajejen shekarar 1985.

A wannan karon ma tafiyar ta taso min ne a dalilin wata hidimar Kasar, watau aikin kula da yadda jarrabawar shiga jami’o’i ta kasa (UTME) take gudana. Tun daga lokacin da aka nada Farfesa Is’haq Oloyede a matsayin Magatakardar Hukuma mai tsarawa da gudanar da jarrabawa domin shiga jami’a a Najeriya (JAMB), a shekarar 2016, ya fitar da sababbin tsare-tsare na yadda ake gudanar da wannan jarrabawar. Daga ciki akwai samar da kwamitoci daban daban, har guda goma sha daya (11), domin gudanar da ayyuka daban daban. Guda daga cikin wadannan kwamitoci shine wanda aka lakabawa suna a Turance da “Roving Group”. Watau kwamiti mai kewayawa santocin da ake gudanar da jarrabawa domin kula da yadda jarrabawar take gudana da nufin gano al’amuran da suke bukatar daukar mataki na gaggawa da kuma wadanda za a zauna a tsanake, a yi musu tunani, a samar da yadda za a ingantasu a shekara mai zuwa. Na sami kaina a cikin wannan kwamiti, a inda na shekara biyu ina aiki a Abuja, shekara guda a Adamawa, shekara uku a Kano, bana kuma aka bukaci na je aiki a Adamawa da Taraba.

Abubuwa uku kwamitin da na yi bayaninsa aka dorawa nauyin kula da su, kamar haka:

1. Yanayin tsaro a ciki da kewayen wurin jarrabawa (CBT Centre); saboda Farfesa Oloyede ya karbi aiki a yayin da a ake cikin kamarin kalu-balen tsaro akasa, musamman na ‘yan Boko Haram;

2. Yanayin tantance dalibai masu zana jarrabawa; saboda amfani da fasahar zamani na tantance masu zana jarrabawa (biometrics) da aka shigo da shi; da kuma

3. Yanayin da dakunan da ake gudanar da jarrabawar suke ciki, da inganci da yalwar na’urori masu kwakwalwa (computers); saboda sababbin santoci masu zaman kansu da aka yiwa rajista ta gudanar da jarrabawar.

Amman fa ba akan wannan aikin zan yi bayani ba, saboda aiki ne da ya shafi hukuma, kuma duk wani bayani ita ake turawa ita kuma ta fitar da wanda ya shafi al’umma ta rike na rikewa. Na dan yi wannan tsokacin ne domin a san dan kadan daga irin hidimar da ake yiwa jarrabawa. Zan yi wannan dan takaitaccen rubutun ne akan abubuwa guda biyar:

1. Tsarin daukar fasinja a tasha
2. Halin da wasu tashoshin mota
 suke ciki

3. Halin da titunan Najeriya suke ciki a shekara ta 2023

4. Yanayin tuki da yanayin larurar bukata a yayin tafiya

5. Yanayin tsaro da alakar jami’an tsaro da direbobin mota.

Babban burina da wannan rubutun shine fata da nake da shi na ko Allah ya sa masu ruwa da tsaki su ci karo da rubutun kuma ya sa su inganta al’amura game da abinda ya shafi tafiya a motar haya a Najeriya.
Manya daga cikin masu ruwa da tsaki kuwa sun hada da Kananan Hukomomi (Local Government Authorities), Kungiyoyin sufuri, da na mamallaka motocin haya, da na direbobin haya, da na ‘yan kamasho, da kuma jami’an tsaro, da sauransu. Zan yi kokarin takaita bayani domin gudun kosarwa. Kuma zan raba posting din kashi kashi duk dai saboda gudun kosawa.

(Za a cigaba da magana akan Tsarin Daukar Fasinja a Tashar Mota, da yardar Allah) 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki