Wike Ya Bawa Ma'aikata Hutu Domin Tarbar Tinibu A Ribas

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu domin tarbar zaben shugaban kasa, Bola Tinudu a ziyarar da zai kai jihar.

Wike, wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne da ke takun saka da dan takarar shguaban kasa na jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, ya ce yayin ziyarar aikin ta kwana biyu, Tinubu zai kaddamar da gadar sama da ginin zamani da ya gina wa kottun Majistare a birnin Fatakwal, hedikwatar jihar.

DAGA LARABA: Yadda Iyaye Ke Kashewa ’Ya’yansu Aure A Arewa
La Liga: Barcelona ta yi wa Osasuna gida da waje a bana
Wike wanda ya juya wa Atiku baya a zaben da Tinubu ya lashe, ya ce, “Ina kira ga daukacin al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwato su yi wa zabebban shugaban kasarmu kuma abin alfaharimu, Mai Girma Sanata Bola Ahmed Tinubu gagarumar tarba, tare da bayyana abin da aka san su da shi na karamci yayin a ziyarar da zai kaddamar da muhimman ayyukan ci gaba da za su zama tarihi.

“Saboda haka na ayyana ranar Laraba, 3 ga Mayu 2023, a matsayin ranar hutu domin muane su samu damar fita su yi wa zababben shugaban kasa maraba.

“Hakazalika daga karfe 8 na safe zuwa 3 na yinin ranar shaguna da wuraren kasuwanci da ke kan titin Rumuola zuwa Rumuokwuta a Karamar Hukumar Obio/Akpor za su kasance a rufe.

“Saboda haka ina kira ga kungiyoyin kwadago da hukumomin tsaro su ba da hadin kai su kuma tabbatar da wannan umarni,” in ji Gwamnan Wike, a jawabinsa ga jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa tun a lokacin ziyarar Tinubu na yakin neman zabe a jihar, ya nuna sha’awarsa ta gayyatar sa domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka a jihar

Bayan kammaala zaben kuma ya aika wa zababben shugaban kasan goron gayyata, kuma ya amsa cewa a jihar zai fara  kai ziyarar aikinsa ta farko bayan zabe.

AMINIYA /NAD 




Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki