Zamu Yi Jigilar Maniyyatanmu Kamar Yadda NAHCON Ta Tsara- Muhammad Awwal Aliyu

Sakataren zartarwar ya ce jihar ta kammala dukkan shirye-shiryen jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ibada ta wannan shekarar, ya kuma yi kira gare su da su jajirce wajen gudanar da horon da ke ci gaba da gudanarwa a fadin jihar domin bitar zata taimaka musu wajen fahimtar da su ayyukan Hajji.

A sanarwar da jami'in hulda da jama’a na hukumar, Hassan Aliyu ya sanyawa hannu, ta ce Alhaji Awwal Aliyu, ya kuma yi kira ga maniyyatan da su tabbatar sun bi dukkan dokokin kasa mai tsarki kamar yadda ma’aikatan hukumar suka fada yayin da hukumar ke jiran lokacin tashi daga hukumar NAHCON.


Idan dai za a iya tunawa, Kamfanin Jiragen Sama na Saudiyya (Flynas) shi ne jigilar Alhazai a Jihar Neja a hukumance.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki