Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na Biyu


 


Daga Dr Sa'idu Ahmad Dukawa

TSARIN DAUKAR FASINJA A TASHA

Bayan da na yi tambayi game da tsarin daukar fasinja a tashar mota, na sami bayanin cewa mutum zai iya zuwa tsahar Na’ibawa (wacce a yanzu aka sakawa suna “tashar Kano Line”) ya yi booking (biyan kudi kafin ranar tafiya). Don haka sai na je ofishin Adamawa Sunshine (wanda alal hakika shago ne a cikin tashar da dan teburi da mutumin da yake karbar kudi ya rubuta rasiti), na biya kudina ana kashegarin ranar tafiya.

Na tambaya mutum nawa ake dauka a mota kirar sienna? Aka ce min ana daukar mutum takwas ne, fasinja biyu a gaba, uku a tsakiya, uku a karshe. Amman fa Bature ya yi motar ne domin daukar fasinja biyar: guda a gaba, biyu a tsakiya, biyu a karshe. Don haka ana wuce kima (overload) na mutum uku. A motar ‘yankasuwa kuwa har mutum hudu ake sakawa a tsakiya, kamar yadda na ganewa idona a yayin dawowata daga Jalingo zuwa Kano. Allah ya kiyaye, a duk lokacin da aka gamu da hadari, za ta yiwu a yi asarar rayuka tara zuwa goma a cikin mota guda. A inda aka san kimar rai, duk yadda za a yi a rage asarar rai guda ana yi.

Ko me yasa dole sai an yi overload a motocin haya a Najeriya? Dalilan sanannu ne. farko dai akwai tsadar man fetur. Na biyu akwai biyan haraji hawan hawa, hukuma ta karba, kungiyoyi su amsa, yan kamasho su yaga, a dankawa ‘yan wururu masu taro fasinja daga hanya su kawo shi gindin mota, a dankawa masu gadin tasha, a yi ta mikawa jami’an tsaro kashi kashi (na kidaya shingen jami’an tsaro kimanin dozen guda a tsaknin Jalingo da Gombe kadai). Ga kuma tsadar kayan mota (spare parts) tunda kusan komai sai an yi odarshi, ba a kera komai a kasar. Ga mamallakin mota yana so ya mayar da kudinsa da wuri, don haka yana son a rika kawo balance mai tsoka a duk rana.

A karshe ga bukatar Direban motar na ya samu abinda zai shiga gida da shi ya sallami iyali. Idan aka hada duk wadannan bukatun akan fasinja kuma ba zai iya dauka ba. Don haka akan dole ake gwammacewa a cunkusa fasinja, wani a jikin wani, kamar kifin sardine.

Akwai kuma abinda yake ya shafi dabi’a ta rashin tsari da ci da zuci da rashin ganin kimar dan Adam wacce take tattare da mutane da yawa, barin idan sun san babu wata doka za ta hau kansu. Alal misali, na biya kudin kujera uku na tsakiya yayin da zan tafi, saboda tare da iyali zan yi tafiyar.

Amman ko da muka zo tasha sai muka taras an cushe wurin ajiyar kaya, babu inda zamu saka ‘yan kananan jakunkunanmu kwara biyu, wadanda idan mun yi tafiya a jirgin sama ba ma auna su, da su muke shiga jirgi, saboda karancin girma ko nauyi da suke da shi. Sai aka nemi wai tunda mu biyu ne kacal a tsakiya, wurin zai ishemu har kayanmu. Ni kuma nace ban amince ba. Daga dukkan alamu kuma sun riga sun sayar da wurin ajiyar kayana, sun karbi sakon kaya wanda shima na samu labarin kudin kujera ake biyansu. Na duba rasitin da aka bani ko akwai lambar wayar ofis sai na kai korafi sai naga in banda sunan na “Adamawa Sunshine” babu komai a jiki, babu lambar waya, babu adireshi! A karshe dai sai saukemu aka yi daga motar, ni da iyalina, na jira wata ta yi lodi bayan sa’a uku, sannan muka kama hanya.

A nan akwai bukatar ace daga cikin jerin masu karbar kudin shiga akwai wadanda suke sa ido wajen ganin an bi ka’ida, an cika alkawari, ko Allah ya sa albarka a harkar da kuma a rayuwarmu baki daya. Wasu shawarwarin da za su biyo baya da za su karfafi wannan, da yardar Allah.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki