'Yan sandan Najeriya sun ceto mutane 58 daga hannun 'yan bindiga
‘Yan sanda a Najeriya sun ce sun ceto mutane 58 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Kogi, yayin da daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da sun ya rasa ransa yayin artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’addan
A cikin wata sanarwa da kakakin rundinar ‘yan sandan jihar Josephine Adeh ta fitar a wannan Lahadin, ta ce wannan nasara da suka samu wani bangare ne na aikin hadin gwiwa tsakanin rundunar da sauran jami’an tsaro, tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarautan jihar.
Adeh ta ce lamarin ya faru ne a dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu mai nisan kilomita 145 daga bababban birnin tarayya kasar.
A cewarta, an yi musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da kuma jami’an tsaro kuma daga bisani suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
Sai dai bata bayyana inda aka sace mutanen ba da kuma tsawon lokacin da suka dauka a hannun ‘yan ta’addan.
RFI