Ba Ni Da Gida A Kasar Waje - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba shi da gida a wajen Najeriya.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar wasikar girmamawa daga jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Hugh Montgomery da takwaransa na Sri Lanka Velupillai Kananathan a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.

Buhari ya ce “A daya daga cikin ganawarmu da Sarki Charles III, ya tambaye ni ko ina da gida a Ingila, amma na shaida masa cewar ba ni da gida a wajen Najeriya.”

Ya kara da cewa, an shafe shekaru da yawa ana musayar al’adu ta hanyar ilimi da horarwa tare da Birtaniya, inda ya nuna cewa ya samu horon soji a makarantar Mons Officer Cadet da ke Aldershot a Ingila 1962 zuwa 1963.

Buhari ya shaida wa jami’in diflomasiyyar Birtaniya cewa kyakkyawar fahimtar banbance-banbancen al’adu, da mutunta cibiyoyi shi ne ya share fagen yawan nasarorin da Birtaniya ta samu.

Ya ce jami’an diflomasiyyar da suka gabata sun kulla alaka da Sarkin Musulmi, Sarkin Kano, Shehun Borno da Sarkin Ilorin.


Shugaba Buhari ya kuma umarci Montgomery da ya ci gaba da kiyaye kyawawan manufofin diflomasiyya, kamar yadda magabata suka yi, ta hanyar mutunta cibiyoyin gargajiya a Najeriya.

Ya ce dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da Sri Lanka za ta kara inganta tare da la’akari da al’adun gida, sarakunan gargajiya, da sauransu.

“Ina jin dadin yadda ake girmama sarakunanmu da hukumominmu, duk da sauyin zamani, ilimi, da karuwar son abin duniya.

“Akwai abubuwa da yawa da za mu koya daga al’adunmu, kuma cibiyoyin gargajiya su ne masu kula da su, kuma ya kamata kowa ya mutunta su,” in ji Buhari.

Ya shaida wa jakadan Birtaniya cewa, huldar diflomasiyyar da ta shafe shekaru da dama tana ci gaba da dorewa bisa mutunta al’adu za ta kara karfi.

A nasa bangaren, Montgomery, ya ce Birtaniya a kodayaushe tana girmama Najeriya da al’adunta, yayin da ya bayyana fatan alheri ga Sarki Charles III, a daidai lokacin da Najeriya ke shirin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Shi ma a nasa jawabin, jakadan Sri Lanka ya shaida wa shugaba Buhari cewa kasar za ta ci gaba da bai wa sojojin Najeriya kwarewa da gogewa wajen yaki da ta’addanci.
AMINIYA 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki