Za Mu Yi Fito-Na-Fito Da Gwamnati Kan Cire Tallafin Man Fetur - Kungiyar Kwadago

Kungiyar kwadagon Najeriya ta sha alwashin yin fito na fito da gwamnatin kasar a kan yunkurin da sabon shugaban Najeriyar ke yi na janye tallafin mai.

Kungiyar ta ce ba za ta amince ba, saboda janye tallafin zai jefa al'umma a cikin wahala.

Tun bayan sanarwar da shugaba Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi aka fara dogayen layukan mai a sassan kasar.

Kwamarade Nasir Kabir shi ne sakataren tsare-tsare na Kungiyar NLC ya shaida wa BBC cewa shugaban Najeriyar ya yi hanzarin sanar shirin cire tallafin man fetur ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

"Kafin ka janye tallafi sai ka kawo wutar lantarki, tituna duk sun wadata talakawa sun rabu da talauci a kasa, ake maganar gwamnati ba ta hannu a cikin wannan abu", in ji shi.


Kungiyar ta yi ikirarin a cikin sa'o'i bayan sanarwar shugaban kasa alummar kasar sun tsinci kansu cikin wani hali na tsaka mai wuya saboda an fuskanci karancin man fetur a wasu sassan kasar da karin farashin mai inda a wasu wurare gidajen mai farashin man fetur din ya karu da kashi 300 cikin 100.

Mahukuntan kasar sun sha ikirarin cewa wasu tsiraru ne ke amfana da tallafin man, don haka yakamata a cire shi .

To sai dai NLC ta yi watsi da haka kamar yada Kwamarade Nasir Kabir ya bayyana:

"Duk wannan magana ne ina tabbatar maka tatsuniya ce, ba mu gamsu da shi ba, ai maganar gaskiya shi ne me ya sa su gwamnatin da ta shigo da ke son ta janye wannan tallafi, da mun zauna mun nuna mu su aubuwan da ke kasa, sai su gane cewa mun fi su gaskiya sai su fasa", in ji shi.

Kungiyar kwadagon ta ce tana adawa da wannan mataki na shugaba Tinubu kuma ta nemi gwamnati da ta janye shirin cikin gaggawa.

NLC ta kuma yi ikirarin cewa abubuwan da wannan mataki zasu haifar za su yi illa ga fanin tsaro da walwalar jama’a.

Hon Abubakar Yunus É—an majalisar wakilai daga Gombe ya shaidawa BBC cewa dawainiyar ta fi karfin gwamnati, kuma talakawa ba sa amfana da tallafin man.

"Ai mun jima muna kira ga tsohon shugaban kasa Muhamadu Buhari da lallai ya janye tallafin.

"Mun kawo korafe korafe a kan cewa tallafin nan in banda cutar da jama'ar da suke kuka a yanzu, ai gara ma a cire shi.

"Da sun san badakalar da babakere da ake yi mu su a wannan harka ta subsidy,…ko da za su yi azumin wata guda da sun amince a cire shi".

Batun janye tallafin dai a yanzu shi kowa ke tattaunawa a kai, fatan 'yan Najeriya dai shi ne samun rangwame daga hauhawa farashin da wasu ke ganin babu mamaki ya karu da wannan sabon tsari.

BBC Hausa 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki