Abun Da Tinibu Da Kwankwaso Suka Tattauna A Kasar Waje


Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa.

Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje.

A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karbi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa hudu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na kasar Faransa.

Majiyarmu ta ce a yayin ganawar, Tinubu ya bukaci hadin kai domin aiki tare da Sanata Kwankwaso — wanda ya lashe kuri’un Jihar Kano a zaben 2023.
Kwankwaso da shugaban kasar da ke jiran rantsarwa nan da mako biyu masu zuwa sun kuma amince za su ci gaba da tattaunawa kan wannan batu.

Majiyar ta ce mai dakin Kwankwaso da zababben Sanata Abdulmumini na Jam’iyyar NNPP ne suka raka madugun Kwankwasiyya zuwa wurin ganawar.

A bangaren Tinubu kuma, matarsa, Sanata Oluremi da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai mai barin gado, Femi Gbajabiamila, ne suka raka shi.

Majiyar ta ce “Matar Tinubu, Sanata Oluremi ce ta karbi bakuncin Hajiya Hafsa, a yayin da ‘yan siyasar kuma suka dauki tsawon lokaci suna tattauna a kan hadin kan kasa da abubuwan da sabuwar gwamnati za ta ba wa muhimmanci.

“Sauran sun hada da batun shugabancin Majalisar Dokoki ta Kasa da kuma aniyar zababben shugaban kasan na kafa gwamnatin hadin kan kasa da ake fatan damawa da Kwankwaso a ciki.

“Sun kuma yi waiwaye a kan kawancensu na siyasa tun suna lokacin da suke Majalisar Dokoki ta Kasa a shekarar 19992,” in ji majiyar.

Majiyar ta kara da cewa a yayin zaman an kuma fara tunanin sasanta tsakanin Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, wato Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje.

A shekarar 2015 Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso, amma ba da jima ba daga baya suka raba gari, kuma har yanzu ba sa ga-maciji.
AMINIYA 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki