Yajin aikin likitocin Najeriya ya jefa majinyata a halin kunci


Tarin asibitoci a sassan Najeriya sun fada halin garari saboda karancin likitocin da ke duba marasa lafiya sakamakon yajin aikin gargadin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD ke yi kasar, inda bayanai ke nuna cewa tuni majinyatan da ke bukatar kulawar gaggawa suka sauya akalar duba lafiyarsu zuwa asibitoci masu zaman kansu sakamakon cunkoson da ake gani a asibitocin gwamnati.


A larabar da ta gabata ne mambobin kungiyar ta NARD suka tsunduma yajin aikin a wani yunkuri na nuna bacin ransu game da rashin cika musu alkawuran da ke tsakaninsu da gwamnati ciki har da karin albashi da akalla kasha 200.

Sai kuma yunkurinsu na kalubalantar kudirin dokar da ke gaban Majalisar kasar da ke shirin kange daga fita ketare don yin aiki har sai bayan sun yi aikin shekaru 5 a cikin Najeriya.

Haka zalika kungiyar likitocin na bukatar gwamnatin Najeriyar ta biya mambobinta bashin kudaden albashin da suke binta tun shekarar 2015 baya daukar tarin ma’aikatan bangaren lafiya saboda karancin ma’aikata a sashen.

Cikin kwana 3 da faro yajin aikin, tuni marasa lafiya suka fara ji a jikinsu saboda rashin likitocin da ke duba lafiyarsu, musamman a biranen da suka kunshi Abuja da Lagos da kuma Kano.

Yanzu haka dai gwamnati Najeriya ta bakin Chris Ngige ta fara tattaunawa da shugabancin kungiyar ta NARD ko da ya ke kungiyar ta musanta.

RFI 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki