Ana Rade-radin Muhuyi Magaji Zai Koma Shugabancin Hukmar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Kusan shekara biyu ke nan Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Muhuyi Magaji Rimingado, daga shugabancin hukumar nan ta Karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar.

Tun bayan dakatarwa Muhuyi da Gwamnatin Kano ke fafatawa a kotunan kasar nan inda Muhuyi ya yi nasara akan Gwamnatin Kano, inda har kotun ma'aikatan wato National Industrial Court ta ce har yanzu Muhuyi ne halartaccen Shugaban Hukumar tare da bayar da umarnin biyansa albashinsa tun daga ranar da aka dakatar dashi har zuwa lokacin yanke hukuncin.

Tuni dai Gwamnatin Kano Mai barin gado bisa talastawa kotu ta biyashi albashinsa.

Ganin Muhuyi cikin kwamitin dawo da kadarorin Gwamnati na Karbar mulki ya sa mutane keta rade-radin dawowar tasa hukumar, amma ziyarar da ya kaiwa Engr Abba Kabir Yusuf yau ta ƙara karfin wannan Rade-radi.

Mutane na ganin Muhuyi Magaji a matsayin Wanda yafi kowa Cancanta da shugabancin wannan hukuma kasancewa aikin da yai a baya tare da ganin cewar yasan da yawa daga cikin badakalolin da akai a wannan Gwamnati Mai shudewa.

Abin jira a gani shi ne ko Gwamnatin Kano za ta dawo da Barrister Muhuyi Magaji Rimingado shugabancin Hukumar?
Hantsi24

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki