Search This Blog

Saturday, 6 May 2023

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana karshen annobar Covid-19

A jiya Juma’a ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kawo karshen annobar Covid-19, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da wargaza tattalin arziki da sha’anin zamantakewar duniya, sama da shekaru 3 bayan da ta ayyana ta a matsayin annoba. 

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da haka a jiya Juma’a, inda ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na nan a matsayin barazana.

Wannan mataki na hukumar Lafiyar na zuwa ne bayan da kwamitin kwararru mai zaman kansa da ta nada a game da wannan cuta ta Covid ya ce cutar ba a bukatar mayar da hankali sosai a kan cutar daga hukumar.

Sai dai a cewar Tedros, hatsarin cutar bai kau ba, inda ya yi kiyasin cewa ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya, kimanin ninki 3 na mutane kusan miliyan 7 da aka ce ta kashe a hukumance.

A ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020 ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar Covid-19 a matsayin annoba, makwanni bayan da ta bulla a birnin Wuhan na kasar China.
RFI 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Head of Service Urges Civil Servants to Uphold Ethical Conduct

The Head of Service, Kano State, has called on civil servants to strictly adhere to the Civil Service ethical code and show grea...