Labari da dumiduminsa : Ganduje Ya Rushe Dukkanin 'Yan Majalisar Zartarwarsa

Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin Kano ya fitar mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ofishin Bilkisu Shehu Maimot

Sanarwar ta kuma bukaci masu mukaman Siyasa da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan Sakatarorin gwamnatin ko daraktoci ma’aikatunsu tare da kayan gwamnati dake wurinsu.

” Wadanda mukamin da aka basu yana da wa’adin sauka to su cigaba da rike mukamansu dai-dai da yadda dokokin da suka nada su suka tanada”. A cewar sanarwar

Sanarwar ta godewa daukacin wadanda suka rike mukaman saboda irin gudunmawar da suka baiwa gwamnatinsa da kuma irin nasarorin da ya samu tsahon shekaru 8 da suka gabata.


Sanarwar ta ce ajiye mukaman ya hadar da kwamishinoni da masu baiwa gwamna shawara da mataimakan gwamna na musamman da manyan mataimaka na musamman ga gwamna da duk Masu rike da mukaman Siyasa.

Idan za’a iya tunawa a ranar Litinin 29 ga watan mayu za’a rantsar da sabon zaÉ“aÉ“É“en gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki