An faɗa mana ƙarasa ayyukan da wasu suka faro babbar nasara ce - Zaɓaɓɓun gwamnoni
An faɗa wa zaɓaɓɓun gwamnonin da za a rantsar ranar 29 ga watan Mayu a Najeriya, cewa a cikin nasarar shugabanci, akwai ƙarasa ayyukan da magabatansu, suka faro.
Matakin zai taimaka wajen tabbatar ci gaban ƙasa da alkinta dukiyar al'umma da rage kashe kuɗi wajen gudanar da harkokin mulki a matakan jihohi.
Wannan jan hankalin, na cikin ɗumbin bayanai da shawarwari da aka gabatar wa zaɓaɓɓun gwamnonin Najeriya, yayin wani taron sanin makamar aiki da aka shirya musu a babban birnin ƙasar, Abuja.
Manufar taron na kwana uku, ita ce shirya gwamnonin masu jiran gado da dabaru da hikimomin shugabanci kafin a rantsar da su nan da kwana 12.
Ƙungiyar gwamnoni ta Najeriya ce ta shirya taron a Abuja, inda ta gayyato ƙwararru a fannoni daban-daban game da sanin dabarun shugabanci a ciki da wajen ƙasar domin bunƙasa ƙwarewar sabbin gwamnonin.
Jiga-jigan 'yan siyasa kamar Simon Lalong na jihar Filato da Nasiru El-rufa'i da su Kayode Fayemi sun ja hankalin zaɓaɓɓun gwamnonin da za su hau karagar mulkin jihohi su fifita muradan al'umma a kan bambancin siyasa da ta aƙida.
Haka zalika, an ja hankalin sababbin gwamnonin kada su yi ƙasa a gwiwa wajen koyon dabaru da salon ayyukan raya ƙasa daga wasu jihohi, don hanzarta ci gaban jihohinsu.
Ɗaya daga cikin mahalarta taron, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu ya ce horon sanin makamar aikin, ba shakka zai taimaka wajen inganta gudanar da harkokin mulki a jihohi da zarar sun fara aiki.
Ya ce "kusan in ce mun koma aji. Don aji ne ake shiga tun bakin ƙarfe 9 na safe zuwa 9:30, wata ran a kai ƙarfe 4 ko 5 na yamma".
A cewar Ahmed Aliyu, duk da yake ya yi mataimakin gwamna tsawon shekara huɗu, kuma ya sha gudanar da ayyukan da gwamna ke yi, amma ya koyi sabbin dabaru da bai taɓa samu ba a baya.
"Musamman an nuna mana muhimmancin ƙarin hanyoyin samun kuɗin shiga a jihohinmu.
Kuma an ja kunnenmu game da buƙatar kammala ayyukan da gwamnoni masu barin gado suka faro, saboda da kuɗin jihohinmu ake yinsu", in ji zaɓaɓɓen gwamnan na Sokoto.
A ranar 29 ga watan Mayun nan ne, za a rantsar da su, bayan zaɓen gwamnoni a ranar 18 ga watan Maris.
Zaɓaɓɓun gwamnonin za su jagoranci jihohinsu ne tsawon shekara huɗu mai zuwa.
Taken horon “Shugabanci Don Ganin Tasiri: Gina Matakan Mulki a Ƙasa” na da burin ƙarfafa gwiwar sabbin gwamnonin wajen lalubo mafita ga matsalolin da za su fuskanta.
A cewar ƙungiyar gwamnonin ƙasar (NGF) wata manufar taron ita ce faɗakar da sabbin gwamnonin irin girman nauyin da zai rataya a wuyansu na amanar talakawa da kuma hanyar da ta fi dacewa su bi wajen sauke wannan nauyin.
Daraktan watsa labarai na ƙungiyar ta NGF, Abdurrazak Barkindo ya ce da ma an saba gudanar da taron don sanar da zaɓaɓɓun gwamnoni da waɗanda suka ci zaɓe wa'adi na biyu game da wahalhalun rayuwa da mutanensu ke ciki da kuma hanyoyin da za su tunkari matsalolin.
Abdurrazaƙ Barkinɗo ya ce yayin taron ana tafka muhawara da gabatar da maƙaloli da kuma musayar ra'ayoyi da gogayya da wasu fitattun shugabanni da suka yi mulki.
A cewarsa, ƙungiyar ta gayyato ƙwararru daga cikin Najeriya waɗanda suka haɗar da tsoffin gwamnoni da wasu ƙwararru da masana daga ƙasashe kamar Kenya da Amurka da sauransu.
Ko da yake, galibi wannan horon ya karkata ne kan yadda za a haɓɓaka tattalin arziƙi da kyautata shugabanci a matakin jihohi, akwai matsaloli da dama shimfiɗe a ƙasa cikin jihohin da sabbin gwamnonin za su karɓi ragamarsu nan da 'yan kwanaki.
Kamar dai na rashin tsaro da kantar talauci da rashin aikin yi da dimbin bashi da kuma rashin biyan hakkokin ma’aikata masu ci da wadanda suka yi ritaya da dai sauransu.