Gabanin Rantsuwa: Zababben Gwamnan Kano, Abba Gida Gida Ya Bayyana Kadarorinsa
Gabanin kaddamar da taron a ranar Litinin, zababben gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, (wanda aka fi sani da Abba Gida Gida) ya bayyana kaddarorin sa da kuma bashin da ake bin sa a cikin fom din da ya cike ya mika a ranar Juma’a ga ofishin hukumar da'ar ma'aikata dake Kano
SOLACEBASE ta rahoto cewa Abba wanda ya samu tarba daga Daraktar hukumar ta jihar Kano Hajia Hadiza Larai Ibrahim, ya bayyana cewa kwazonsa na bayyana kadarorinsa nuni ne na gaskiya da rikon amana da zai zama ginshikin gwamnati mai zuwa a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sunusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce: "A yau, na cika hakkin da kundin tsarin mulki ya dora min na bayyana kadarorina kafin na shiga Ofis, ranar 29 ga Mayu."
''Zababben Gwamna, ya shaida wa mata cewa aikin gwamnati kira ne; hidima ce ga bil’adama kuma a shirye nake a koyaushe in yi hidima bayan samun amincewar mutanen jihar Kano, in ji sanarwar.
''Bugu da kari, Engr. Abba ya bayyana cewa a halin yanzu haka komai ya fito fili don tafiyar maido da ci gaba mai dorewa a dukkan bangarori, inda duk wani Kobo na asusun gwamnati da aka kashe ba kawai zai zama ta hanyar rashin gaskiya ba, har ma a jihar Kano karkashin kulawar sa.
‘’Ya ba da tabbacin cewa dukkan jami’an gwamnati da suka hada da masu rike da mukaman siyasa da za su yi aiki a gwamnatinsa za a ba su izinin bin tsarin bayyana kadarorin kamar yadda doka ta tanada.