Al'ummar Turkiya za su kada kuri'a a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa
A karon farko al’ummar Turkiya na shirin kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, bayan koma bayan da shugaba Recep Tayyib Erdogan ya samu da ya hana shi iya lashe zagaye na farko na zaben duk kuwa da tazarar yawan kuri’u.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan da ke jagorancin Turkiyya tun daga shekarar 2003, wannan ne karon farko da sakamakon zabe ke nuna ya gaza samun kasha 50 na yawan kuri’un da aka kada duk da cewa akwai gagarumar rata tsakaninsa da babban abokin karawarsa.
Gabanin fitar sakamakon zaben, shugaba Recep Tayyib Erdogan yayin jawabi gaban dandazon magoya baya, ya bayyana cikakken shirin da ya ke dashi na sake jan ragamar Turkiya zuwa shekaru 5 a nan gaba.
Erdogan mai shekaru 69 ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsa mai rajin bin tafarkin addinin Islama ta lashe galibin kujerun Majalisa, sai dai alkaluman da kamfanin dillancin labaran kasar ya wallafa sun nuna Erdogan a matsayin wanda ya lashe kashi 49.3 yayinda jagoran adawa Kemal Kilicdaroglu ke da kashi 45.
Wannan sakamako gad an adawa Kemal dai babban koma baya ne lura da yadda kuri’ar jin ra’ayin jama’a gabanin zabe a baya ta nuna shi a matsayin mai rinjaye.
Yanzu haka dai dukkanin bangarorin biyu za su zage damtse don tunkarar zagaye na biyu da aka tsara zai gudana ranar 28 ga watan da muke na Mayu.
RFI