Karin Kudin Tikiti: Za A Dauki Dala 100 Daga Guzurin Alhazai

 


Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce za ta dauki Dala 100 daga cikin kudin guzurin maniyyata aikin Hajjin bana, domin biyan karin kudin kujera da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar su suka yi. 

Yakin da ake yi a Sudan ya sa kasar rufe sararin samaniyarta, don haka dole sai jiragen da za su dauki maniyyatan su bi sabuwar hanya da ta bi ta kasar Chadi da Habasha da Eretiyiya da Kamaru kafin isa kasar Saudiyya.

ِKafin barkewar yakin da ya sa aka rufe sararin samaniyyan Sudan, jiragen maniyyatan Najeriya kan tsallaka ne ta Chadi su shiga Sudan ne kadai kafin su isa Saudiyya.

Wani manaja a wani kamfanin da zai yi jigilar alhazan ya bayyana wa Aminiya cewa, “A duk lokacin da aka tsayin tafiya ya karu to dole kudi su karu saboda man da za a zuba a jirgi ya karu, haka kuma kudin da za a biya ma’aikatan jirgi shi ma ya karu; Hakan ya janyo dole a yi kari a kudin tikitin alhazan.”

Bayan yamutsa gashin baki da kai-kawo a tsakanin Hukumar NAHCON da kamfanonin jiragen a kan karin kudin, a karshe sun amince za a kara Dala 250 ga kowane maniyyaci.

A lokacin, hukumar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin cewa ba a dora karin akan alhazan ba, amma kuma yanzu ta bayyana cewa za ta dauki karin da aka samu na kudin tikitin ne daga kudin guzurin maniyyata.

Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an rage karin kudin tikitn daga Dala 250 zuwa Dala 116, wanda kuma za a cire Dala 100 a guzurin alhazai, ita Hukumar NAHCON ta hukumomin jin dadin alhazai na jihohi za su dauki nauyin biyan Dala 15 a tsakaninsu.

“Kowa ya san cewa an yi tataburza da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar a kan karin kudin tikitin domin da farko sun ce dole sai an kara Dala 500, daga baya aka yi sauki tare da amincewa a kan Dala 250.

“Haka kuma Hukumar NAHCON ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ba a dora wa alhazai biyan wancan karin kudin ba, don haka ta nemi Fadar Shugaban Kasa ta dauki nauyin biyann karin.

“A kan hakan ne Fadar Shugaban Kasa ta rage kimanin kaso 35 na harajin da ke kan kamfanonin jiragen. Hakan ya janyo a yanzu aka sami raguwar karin daga Dala 250 zuwa Dala 116.”

A cewar Abba Dambatta, “zduba da cewa a yanzu lokaci ya kure ba za a iya cewa alhazai su karo wancan karin ba, muka ga ba mafita sai dai a dauka daga cikin kudin guzurin alhazai.

“A takaice dai yanzu za a dauki Dala 100 daga guzurin alhazai na Dala 800, ita kuma ragowar Dala 16 za ta fito daga Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihohi da kuma Hukumar NAHCON.”

AMINIYA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki