Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 3 - Dr Dukawa
A bisa kiyasi, tashar Na’ibawa a Kano ba za ta gaza shekara arba’in (40) ba. Saboda an samar da ita ne a zamanin marigayi gwamnan tsohuwar jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi (1979 – 1983). Amman har izuwa yau tashar tananan jiya ya yau: kango wanda babu wani abu da yake nuna ana samun kudi a wurin; babu kwalta, babu interlocks, babu dabe kowane iri! Zaiyar kasa. Sai yalwar leda da sauran nau’i na shara. Babu wani lafiyayyen makewayi. Da na bukaci wurin yin bawali sai aka nuna min wani uban juji a yammacin cikin tashar. Sai da roki wani dan bola jari cewar ya dan kauce zan kama ruwa.
Na tabbatar idan ruwa ya sauka mummunan halin da tashar ke ciki ba zai gaza na tashar Unguwa Uku ta Kano ba, wacce na yi rubutu akan nata halin da take ciki a sherarar 2020.
An yayyanka pilotai a cikin tashar Na’ibawa. Wasu an gina shaguna ana gudanar da ciniki wasu kuma an saka fandisho na gini ba a yi ginin ba. Babu Masallaci sai ‘yar musalla amman har da lasifika. Ko yaya aka yi a kasar Musulmi irin Kano za a yi tashar mota ta shekara arba’in ba a samar da masallaci ba sai abin ya daurewa mutum kai. Alhali ya kamata ace izuwa yanzu har dakin shan magani, da karamin dakin ATM da ofishin aika sako (akwatin gidan waya) na gaggawa, da kuma ofishin ‘yansanda ya kamata ace an samu.
Halin da na samu tashar mota a Yola da Jalingo bai sha banban da yadda na baro a Kano ba. Babu wani abu na cigaba. Sai turbaya da shara da bola.
Anan zan nanata kirana ga kananan hukumomi (LGAs) a Arewacin Najeriya cewar su tuna amanar da suka dauka na gudanar da ayyukan da aka zayyana a makale na hudu (fourth schedule) na Tsarin Mulkin Najajeriya. Daga ayyukansu akwai samarwa da kula da tashoshin mota. Wannan ba ya nufin a shata kango motoci su rika shiga suna lodi ‘yan rabanu (masu karbar kudin shiga) kuma suna karbar haraji kawai ba.
Amman yana nufin a inganta tashoshi ta hanyar samar da yanayi mai kyau da tsabta da tsaro. Kunyoyin da suke karbar nasu kason a wurin direbobi su ma su sani cewar babban aikinsu shine su inganta sana’ar ta hanyar bibiyar hukumomi da neman su sauke nauyinsu da kuma taya hukumomin samar da wasu abubuwan inganta rayuwa a wurin sana’a. sabanin haka za su rika cin haram ne na wannan kudaden da suke karba.