Kotun Senegal ta daure 'yan majalisa saboda dukan mace

 


Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a kan ‘yan majalisar dokokin kasar su biyu na bangaren 'yan adawa, saboda samun su da laifin dukar abokiyar aikinsu daga bangaren masu rinjaye.

A ranar 1 ga watan Disambar da ya gabata ne dan majalisar dokoki Massata Samb ya yi dirar mikiya a kan wata ‘yar majalisar mai suna Amy Ndiaye, bisa zargin furta kalaman batanci a kan Moustapha Sy, shugaban wata jam’iyyar siyasa da ke cikin gungun ‘yan adawa sannan kuma shehin malamin addinin musulunci da ake mutuntawa a kasar.

Wasu hotuna da ake rika yadawa sun nuna yadda Massata Samb ya lafta wa Amy Sy mari a cikin zauren majaliar ‘yayin da abokinsa dan majalisa Mamadou Niang ya sa kafa ya noshi matar a ciki bainar jama’a.

Bayan faruwar wannan lamari, an kwantar da ‘yar majalisa Amy Sy a asibiti bayan da bayanai suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin, to sai dai a lokacin da yake yanke hukunci, alkali ya yi watsi da zargin yunkurin kisa kamar dai yadda masu shigar da kara suka bukata.

Ko baya ga hukuncin dauri, hakazalika kotun ta bukaci mutanen biyu su biya tarar cfa jika dari a matsayin diyya saboda dukar da suka yi wa ‘yar majalisar wadda ta fito daga jam’iyyar shugaba Macky Sall.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki