Labari da dumiduminsa :Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Da Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado Kan Mukaminsa
Mai Girma Alh. Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jihar Kano, ya amince da mayar da Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa, PCACC, domin kammala wa’adinsa.
Za a Iya tuna cewa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barr Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.
Sanarwar da babban sakataren Yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Mayar da shi mukaminsa ya fara aiki ne nan take bisa bin umarnin da Kotu ta bayar tun a baya cewa gwamnatin ta mayar da shi