Babu Wurin Buya Ga Masu Aikata Laifuka A Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ganin ta kawar da duk wasu miyagun da suka addabi al’ummar jihar tare da tabbatar da cewa jama’a na gudanar da ayyukansu lafiya.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci hukumar tsaron farin kaya ta kasa (NSCDC) na jihar, inda ya ga yadda aka yi holar masu aikata laifuka da dama da jami’an rundunar suka kama tare da baje kolin makamai da kayayyakin da aka kwace daga hannunsu.

A cewar Gwamnan; “Dole ne hukumar NSCDC ta jihar ta gurfanar da ku a gaban kotu sannan bayan wa’adin gidan yari, wadanda suka tuba kuma suka yi nadama, za a gyara halinsu tare da shiga cikin al’umma kuma za a ba su ikon dogaro da kai. .

Gwamnatinmu ba za ta lamunci lalata ko wace iri ba Daga matasanmu domin ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka dace kan duk wanda aka samu yana son samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.” Inji Gwamnan.

A nasa jawabin, Kwamandan hukumar na jihar, Muhammad Lawan Falala ya ce an kama wadanda ake zargi 19 da aka kama bisa laifuka daban-daban da suka hada da; Satar waya, lalata, sata da dai sauransu suna tabbatar da cewa za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki