Hukumar Alhazai Ta Kano, Ta Ce Kar Wani Maniyyaci Ya Ji Firgicin Cewa Ba Zai Je Aikin Haji Ba
Hukumar kula da Jin dadin alhazai ta Jihar Kano, ta ce Rashin Tafiya zuwa aikin Hajji Da Wuri, Ba Yana Nufin Ba Maniyyata Ba Za'a Yi Hajjin Bana Ba Dasu , Kamar Abun Da Ya Faru Waccan Shekarar.
A sanarwar da sashen Yada labarai na hukumar karkashin jagorancin Yusuf Abdullahi ta fitar, hukumar tace Kar Wanda Yaji Tsoro Ko Firgici A Ransa Cewa Baze Samu Tafiya Ba. Wannan Hukuma Tana Iya Bakin Ƙokarinta Wajen Samar Da Ingattaccen Tsarin Da Ze Tabbatar Da Cewa Ta Sauke Nauyin Da Allah Ya Ɗora Mata.
Hukumar Ta kara da cewa, Duk Wanda Ya Biya Be Tafi Ba Wannan Karo, Toh Gaskiya Muna Kyauta Zaton Yazo Cikin Wadanda Ma'aikatar Baya ta Siyarwa Da kujerun Bogi.
Koda yaushe Za'a Cigaba Da Kira Tare Da ÆŠibar Alhazai Har Sai Ranar Aka ÆŠebe Kowa.
A Saboda Haka, Hukumar Ke Godiya Tare Da Rokon Jama'a da suci gaba da Hakuri tare Da bamu HaÉ—in Kai, kwarin gwiwa, da kuma Tayamu Da Addu'a don Ganin mun sauke nauyin da Allah ya dora mana.