Gwamnan Kano Ya Nada Habu Fagge Shugaban Hukumar Amintattu Ta 'Yan Fansho

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Habu Muhammad Fagge a matsayin shugaban gudanarwa na hukumar amintattu ta 'yan fansho ta jihar Kano.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace nadin ya fara aiki ne nan take kamar yadda gwamnan ya bayar da umarnin mikawa tare da karbar ragamar mulki cikin sa’o’i 24 da wannan sanarwar.

Alhaji Habu Fagge, wanda ya kammala karatunsa na digiri daga Jami'ar Abraham Lincoln, ya yi wa'adi biyu a matsayin Shugaban Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano.

Ya rike mukamai daban-daban a ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da suka hada da daraktan kudi, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga da darakta sauran haraji.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki