Bayan Sanarwar Dawo Da Shi Kan Mukaminsa, Barista Muhuyi Magaji Ya Gana Da Ma'aikatan Hukumar

Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya kama aiki.

A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Yusuf Abubakar Ibrahim ya sanyawa hannu, tace Za a iya tunawa a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labari, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano domin ya kammala wa’adinsa bisa ga umarnin Kotu.

Barista Rimin Gado ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin dawo da martabar hukumar.

Ya bukaci shuwagabanni da ma’aikatan hukumar da su ba shi dukkan goyon bayan da ake bukata domin cimma burin da ake bukata.

Ya kuma bukaci Ma’aikatan da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu domin zai yi iya kokarinsa wajen tallafa musu.

Da yake mayar da jawabi, Daraktan Kula da Ma’aikata, Mahmud Haido ya tabbatar wa Shugaban Hukumar da duk wani hadin kai da ya dace daga Ma’aikata da Ma’aikatan Hukumar, tare da yi masa fatan samun nasara tare da samun Shugabanci na gari. 


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki