Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu - Abdallah Amdaz
Alhamdulillah, Dalilin da ya saka zanyi magana akan wannan bawan Allah wanda ko saninsa banyi ba shi ne, saboda ya burgeni sosai matuƙa, ma sha Allah gashi matashi, ga karsashi Mallam abun gwanin ban sha'awa, wallahi ni ko sunansa ma ban sani ba, kuma ban damu da in sani ba, kawai dai ko ina yake a faɗin duniya, idan ya samu saƙona ina shaida masa cewa, YAYI DAI-DAI, yaci gaba a haka ake zama abun kwatance a duniya, domin juma'ar da zatai kyau tun daga Laraba ake gane ta.
Abun takaicin shi ne adawa da kin gaskiya da kokarin tozarta dan Adam ya rufewa mutane idanun, suna aibata shi saboda son zuciya, don kawai suna da banbancin jam'iyya, wannan kuskure ne babba, kasarmu da al'ummar mu sune a gaban kowa, in kaga munyi fada dakai kaci mutuncinsu ne, koka danne hakkin su.
Sannan ni Abdallah Amdaz ba yaron kowanne dan siyasa bane, kuma niba karan kowa bane da zaisani nayiwa wanda baya so haushi, ra'ayin kaina kawai nakeyi, don haka inkaga nayi magana akan ka ɗayan biyu ne, kayi dai-dai koka saɓa.
Amma abun takaicin irin yanda naga ana aibata wannan bawan Allah akan wani abun banza wai turanci, sai kunya ta kamani nace wai shin, turanci ake zuwa karewa majalisa ko kuwa haƙƙin talakan ƙasa, nifa a ra'ayina indai kasan me kake kuma in kayi turancin ana dan fahimta, kawai ka wargazo shi wanda ya gane ruwansa.
Yanda wannan bawan Allah, ya iya tsayawa ya kawo motion a gaban majalisa abun alfahari a karonsa na farko a wannan guri, wani abun burgewar ma shi ne, alamunsa sun nuna yasan me yake, ta inda Allah yasa ya iya gano hadarin dake tattare da bawa ɗai-ɗaikun yan kasuwa damar juya kasuwanci ƙasa, wanda wannan abu na iya haifar da monopoly, wanda zai gallazawa rayuwar mutane.
Ni a nawa hangen abunda yayi dai-dai ne, kuma ba haddasa tasa yayi wannan maganar tasa ba, illa yaƙinin da yake da shi cewa ta hanyar hakan za'a samu gyara, idan akayi la'akari da mahimmancin maganarsa, don yayi wani ɗan kuskure ba wani abu bane dama ɗan Adam ne hakan zata iya faruwa akan kowa.
Ni a ganina ba tsangwamarsa da hantararsa yakamata ayi ba, ƙarfafa masa yakamata ayi, tare da bashi goyon bayan daya dace, don ya samu ƙwarin gwiywar sauke nauyin al'ummar da suka zabe shi.
Turanci ba shi ne ilimi ba, ba kuma shike nuna mutum me ilimi bane, turanci hanyace ta isar da sako kawai, akwai da yawan masu ilimin da basu iya turanci ba, basu san tayaya akeyinsa ba, akwai attajirai da masu baiwa ta musamman da basu iya shi ba, kuma hakan bai hana su rayuwa mai inganci ba, ballantana wannan bawan Allah dana saurari turancinsa, mai kyau ne ma sha Allah, kuma ban tarar da kuskure ba, a ɗan karamin sanin sa da nake da shi,, illa kawai kwarjinin majalisar da mutanen dake cikinta, a kasancewarsa ta farko a ciki.
Wannan Dan majalisa ako ina yake ina masa fatan alkairi, tare da addu'ar Allah ya bashi agaji da taimakonsa na jajircewa akan abinda aka zabe shi, Allah ya yawaita mana matasa masu kishin kasa irinsa.