Gwamnatin Kano Ta Kafa Kotunan Tafi Da Gidanka Domin Magance Satar Waya

Gwamnan jihar Kano, Yusuf Abba, ya amince da kafa kotunan tafi da gidanka domin tabbatar da hukunta masu satar wayar a jihar cikin gaggawa.


A wata sanarwa da sakataren yada labaran sa, Alhaji Bature Tofa ya fitar, ya ce kotunan tafi da gidanka za su hada hannu da rundunar hadin gwiwa ta musamman domin hukunta wadanda aka kama.

Yusuf ya ce manyan titunan birnin sun haska ne bayan shafe shekaru takwas na duhu yayin da aka kashe fitulun.

“Mayar da fitilun kan titi na cikin kokarin da sabuwar gwamnati ke yi na magance matsalar fashi da makami da sace-sacen waya da sauran miyagun ayyuka, musamman a babban birnin Kano.

"Aikin da ake ci gaba da gudanarwa ya fara tun ranar Talata kuma zai ci gaba har sai an kubutar da kowane bangare na jihar daga duhun da ke ba da mafaka ga masu aikata laifuka da 'yan bangar siyasa," in ji shi.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki