Anyi kira Ga Tsofaffin Jami'an Alhazai Na Kananan Hukumomin Kano, Su Gaggauta Mika Ragamar Aiki Ga Sabbin Jami'an

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa, yayi wannan kiran ne a Ranar Lahadi, lokacin da yake kaddamar da Sababbin Jami'an a hedikwatar hukumar

Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa wanda ya taya Sababbin jami'an Alhazan murnar zabar su da Allah yayi domin su hidimtawa alhazai bakin Allah yayin gudanar da aikin Hajin bana 

Darakta Janar din wanda ya bayyana cewa yana da yakini kasancewar kusan dukkanin Sababbin jami'an sun taba gudanar da aikin a baya hakan ta sanya yake fatan ba za a samu wata matsala ba cikin gudanar da aikinsu 


Da yake nasa jawabin, Shugaban hukumar alhazai ta jahar Kano, Alhaji Yusuf Lawan, yace gwamnatin Kano karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf ba zata taba lamuntar rashin gaskiya ba, don haka ya ja kunnen Sababbin Jami'an Alhazan da su rike amanar da aka basu. 

Alhaji Yusuf Lawan ya kuma gargadesu dasu kiyayi Karbar kudaden maniyyata da nufin cewar zasu biya musu kudin Hadaya, wanda yace hakan na bawa wasu damar yin ha'inci wanda yace babu wanda gwamnati za ta ragawa idan aka same shi da aikata hakan. 

Ya kuma yi amfani da taron wajen sake godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya basu domin hidimtawa bakin Allah 


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki