Shirin Aikin Hajji Na 2023 Yana Ci Gaba Da Samun Nasara - NAHCON

Aikin Hajjin 2023 daga Najeriya ya shiga kwana na bakwai inda kawo yanzu an samu tashin jirage sama da 33. A jihohin Filato da Benuwai da Nasarawa an kammala jigilar maniyyatan nasu ta jirgin sama yayin da sauran jihohin ma ke samun ci gaba. Idan dai ba a manta ba hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kara yawan jiragenta zuwa biyar a bana.

A sanarwar da mataimakiyar Daraktar harkokin hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara, tace Sai dai hukumar ta NAHCON ta amince da cewa wata matsala ta fasaha ta shafi daya daga cikin jiragen da hukumar ta samu kwangilar jigilar alhazan jihar Jigawa zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023. 

Matsalar da aka samu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, ya tilasta wa jirgin sauka na wani dan lokaci a filin jirgin saman Aminu Kano da ke Jahar Kano.

Yayin da lamarin ya haifar da tsaikon da babu makawa, ko shakka babu shugaban hukumar Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya tabbatar wa alhazan Najeriya musamman wadanda ci gaban da ba zai yuwu ya shafa ba, cewa an yi tafiyar da alhazai yadda ya kamata, kuma ba zai kawo cikas ga zirga-zirgar alhazai ba. 

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, NAHCON ta riga ta kammala shirye-shiryen kawar da duk wani jinkiri ko soke jirgin da zai kawo cikas ga jigilar maniyyata zuwa Saudiyya cikin sauki.

Ya zuwa yanzu kusan mahajjata 14,000 suna cikin koshin lafiya a birnin Madina kuma adadin jiragen da ke jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya ma zai karu nan da kwanaki biyu. Ana gudanar da aikin kamar yadda aka tsara tare da sanya matakan baya a cikin yanayin da ba a zata ba. 

Don haka an umurci alhazai da su kasance cikin shiri a kowane lokaci domin tafiya Saudiyya.

Hukumar NAHCON za ta ci gaba da fadakar da jama’a da bayanan da suka dace kan yadda aikin ke gudana.



Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki