Gwamnatin Kano Ta Nemi Karfafa Dangantaka Tsakaninta Da Kasar Saudi Arabia

Gwamnatin jihar Kano ta nuna sha’awarta na karfafa alakar da ke tsakaninta da kasar Saudiyya domin amfanin gwamnatocin kasashen biyu.

A cewar sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan batu ne a lokacin da ya karbi bakuncin karamin jakadan Saudiyya a Kano,  Khalid Ahmad Al-adamawi tare da kodinetan kungiyar musulmi ta duniya Dr Salisu Ismaila a gidan gwamnati.

Gwamnan ya yaba da ziyarar tare da neman karin tallafin karatu da gwamnatin Saudiyya ke baiwa ‘yan asalin Kano don yin karatu ko kuma ci gaba da karatunsu a jami’o’in Saudiyya.

Alh Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da addu'ar Allah ya tabbatar da burinsa na kafa Jami'ar Kiwon Lafiya da Asibitin koyarwa domin shiri ne wanda a cewar Gwamnan zai dauki nauyin kula da lafiyar jama'a da dama a Kano da Jihohi makwabta da sauran su.

Ya kuma nemi tallafi ta fannin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da rage mace-macen mata masu juna biyu ta hanyar gine-gine da gyare-gyaren ajujuwa da samar da kayan aikin jinya ga makarantun gwamnati da asibitoci bi da bi.

Karamin Jakadan, Khalid Ahmad Al-adamawi ya ce sun ziyarci gidan gwamnati ne domin yi wa Gwamna bayani kan aikin tiyatar bugun zuciya da ake yi a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) wanda kungiyar musulmi ta duniya ta dauki nauyi tare da tallafin Sarki Salman. gidauniyar cewa nan ba da jimawa gidauniyar za ta bude cibiyar tiyatar zuciya a Kano.

Ya kara da cewa, an raba katanan dabino guda 550 ga jama’ar jihar tare da yin alkawarin bayar da karin taimako ta fuskar kiwon lafiya da ruwa.

Ko’odinetan Kungiyar Musulmi ta Duniya a Najeriya, Dr Salisu Ismail ya koka da karancin likitocin zuciya ganin cewa akwai kwararrun likitocin tiyatar zuciya guda 4 a Arewacin Najeriya domin kula da masu fama da ciwon zuciya da yawa lamarin da ya kamata a magance shi sosai.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki