Labari da dumiduminsa : Gwamanatin Kano Za Ta Fara Aikin Tantance Daliban Da Za Ta Dauki Nauyinsu Don Karo Karatu A Kasashen Waje

Gwamnan ya ce "A cikin jawabin da na gabatar ranar rantsuwa, na bayyana cewa mun dawo da tsarin nan na cigaba da bayar da tallafin karatu ga ɗaliban mu na jihar Kano domin samun manyan digiri a cikin gida da ƙasashen waje. 

Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na #Facebook, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da "A cikin watanni masu zuwa, za a fitar da ƙarin bayani, kuma za a fara aikin tantancewa domin fara wannan aiki.

Haka kuma, za a buɗe makarantun fasaha guda 44 da Makarantun koyon Ilimin Addinin Musulunci guda 44 da ke fadin kananan hukumominmu da Gwamnatin Sanata Kwankwaso ta kafa, wadanda gwamnatin da ta gabata ta rufe kuma ta yi watsi da su domin ci gaba da karatu da.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki