Muna Kan Tataunawa Da Kwankwaso Da Obi - Atiku
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata barazana ga damarsa a zaben. “Ban ga wata barazana domin ba ma tare da su (Kwankwaso da Obi). Muna cikin tattaunawa da su, watakila daya daga cikinsu ya zo,” inji shi. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata ba...