Kotu ta umarci Bankin Guarantee Ya Biya N5.7m Da Muhuyi Rimingado Daga Asusun Gwamnatin Kano

Kotun ma'aikata ta kasa da ke Abuja ta umarci Bankin (GT) da ya biya korarren shugaban hukumar KORAFE-KORAFE jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, kudi N5,713,891.22 daga asusun albashi na gwamnatin jihar.

Adadin kudaden da  Rimingado ke bin gwamnatin ne na albashin ma’aikata, bayan dakatar da shi a watan Yulin 2021.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta dakatar da Mista Rimingado ne bayan bude bincike kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan.


A zaman da aka ci gaba da yi a ranar Talatar da ta gabata, Bankin ta bakin lauyansa Joshua Shekwolo ya shaida wa kotun a cikin wata takardar neman sahalewa cewa gwamnatin jihar Kano ta na da asusun ajiyar banki da jimillar kudaden da suka kai N5,713,891.22 kasancewar an toshe hukuncin da aka yanke kan lamarin. a cikin asusun.



Da yake bayar da cikakkiyar umarnin, mai shari’a O.O Oyewumi ya umarci GTBank ya biya kudin a asusun Mista Rimingado cikin sa’o’i 48.

An bayar da umarnin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen mutunta hukuncin da kotun ta yanke a ranar 14 ga Disamba, 2022, inda ta bayar da umarnin biyan da kuma amincewa da Mista Rimingado a matsayin halastacen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki