Adadin mutanen da aka kashe a rikicin Sudan ya kusan 100
Kungiyar likitoci a Sudan, ta ce adadin wadanda aka kashe a fadan da ake cigaba da gwabzawa tsakanin sojojin kasar da jami’an tsaron rundunar musamman ta kai daukin gaggawa wato ‘Rapid Response’, ya karu zuwa mutane 97, cikinsu kuwa har da jami’an majalisar dinkin duniya uku.
Tun a ranar Asabar, rikicin ya barke bayan da aka kwashe makwanni ana takaddama tsakanin hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar dakarun RSF mai karfin fada a ji, wadda shugaba Burhan ke son narkar da ita zuwa cikin rundunar sojin kasar.
Kazamin fadan ya cigaba da yin kamari ne kuma duk da cewar bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaitar wutar wucin gadi a ranar Lahadi, domin ba da damar bai wa wadanda rikicin ya rutsa da su kulawar gaggawa.
Likitoci sun ce daruruwan mutane ne suka jikkata, yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa kusan dukkanin asibitoci 9 da ke birnin Khartoum, basu da jini da kuma ruwa da marasa lafiya ke bukata.
A halin da ake ciki hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP da aka kashewa jami’ai uku, ta dakatar da ayyukanta a Sudan har sai abinda hali yayi.
Tuni dai kasashe da dama suka yi Allah wadai da gumurzun da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun musamman na RSF, yayin da wasu kasashen kamar Chadi da Masar suka rufe iyakokinsu da kasar ta Sudan.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da takwaransa na Birtaniya James Cleverly, sun bayyana matukar damuwa game da kazamin fadan da suka bayyana a matsayin barazana ga makwaftan Sudan ba ma al’ummar kasar kadai ba.
Yau Litinin ake sa ran shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU, Moussa Faki Mahamat, zai isa kasar domin shiga tsakani da jagorantar kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
RFI