Yadda masu son muƙamin shugaban majalisa ke sayen ƙuri'un sanatoci - Ndume

 


A Najeriya bayan kammala zaɓukan ƙasar a yanzu hankali ya karkata kan shugabancin zaurukan majalisun dokoki.

Tuni dai wasu 'yan majalisun da ke son ɗarewa kujerun shugabancin majalisun suka fara bayyana sha'awarsu ta hanyar kamun ƙafa a wajen masu ruwa da tsaki na jam'iyyunsu da kuma zaɓaɓɓun 'yan majalisar.

Sai a watan Yuni mai zuwa ne za a ƙaddamar da majalisar dokokin ta goma, daga nan kuma a fara shirye-shiryen zaɓen shugabannin majalisun.

To sai dai wasu 'yan majalisun sun fara zargin cewa ana amfani da kuɗi wajen sayen bakin 'yan majalisun domin zaɓen wasu a matsayin shugabannin majalisun.

Sanata Ali Ndume ɗan majalisar dattawa ne daga jihar Borno ya kuma shaida wa BBC cewa akwai zargin da ake yi na cewa wasu na amfani da kuɗi wajen ganin sun samu ɗarewar kujerar shugaban majalisar dattawa.

Ya ce a yanzu siyasar ƙasar masu hannu da shuni, ko masu kuɗi su ne ke juya ɓangaren siyasar ƙasar.

''Dandalin siyasarmu ya cika da irin waɗannan mutanen da suke ganin za su iya sayen komai suke so da kuɗi'' in ji Sanata Ndume.

Dan majalisar dattawan ya ce a baya ana maganar cewa ana sayen ƙuri'ar talaka, matakin har ya kai ga talakawan ƙasar suna ganin komai nasu na sayarwa ne a ɓangaren zaɓen ƙasar.

'A yanzu har ƙuri'ar sanata ake saya'

Majalisar Dattawa

ASALIN HOTON,NIGERIAN SENATE

Dan majalisar dattawan ya ce matakin ya kai a yanzu har ƙuri'ar sanata ma ana so a saya.

Ya yi zargin cewa a yanzu masu son ɗarewa kujerar shugabancin majalisar dattawan sun fara sayen ƙuri'un sanatoci.

''Akwai sanatocin da suke bai wa 'yan majalisar dattawa kuɗi a kan suna so su nemi shugabancin majalisar'' In ji Ali Ndume.

Ali Ndume ya ce bayan kwarewa a majalisar, idan mutum yana da kuɗi to damar da yake da ita ta zama shugaban majalisar ta fi yawa.

Sanatan ya kuma yi zargin cewa a yanzu akwai sanatocin da ba su da kwarewa a aikin majalisar, amma suna son mukamin shugaban majalisar dattijai.

''Amma saboda suna da kuɗi, amma yanzu suna son ɗarewa shugabancin majalisar, kawai saboda suna da kuɗi''.

'Kamun ƙafa da kuɗi a maimakon cancanta'

Ali Ndume

ASALIN HOTON,SANATA ALI NDUME/FACEBOOK

Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa ba kawai sanatocin masu muradin shugabancin majalisar ke saya ba, har da sauran hukumomi.

''A yanzu duk abinda kuɗi bai baka ba a Najeriya to sai in kuɗin ne ya gaza, kuma idan ka ƙara za ka samu'', in ji Ndume.

Dan majalisar ya ce abu biyu ne a yanzu suke yin tasiri wajen samun shugabancin majlisar wato da kamun ƙafa da kuma kuɗi, maimakon cancanta.

Sanata Ndume ya kuma yi ƙorafin cewar a yanzu maimakon ya mayar da hankali kan cancanta domin zaɓen shugaban majalisar, an mayar da hankali wajen kamun ƙafa da kuma bayar da kuɗi.

'Ya kamata a bi cancanta maimakon tsarin shiyya-shiyya'

Sanata Ali Ndume ya kuma ce bai ga dalilin da zai sa a bi tsarin shiyya-shiyya a shugabancin majalisar dattawan ƙasar ba, a cewarsa kamata ya yi a bi cancanta.

''A lokacin babban zaɓe na yadda da batun shiyya-shiyya, amma a zaɓen da za a yi tsakanin waɗanda sun riga sun ci zaɓe ban goyi bayan shiyya ba'', in ji shi.

A cewar ɗan majalisar bin tsarin shiyya-shiyya zai haifar da samun shugabannin majalisar waɗanda ba su cancanta ba.

''Akwai wasu fa a majalisar nan waɗanda suna da tabo na laifi, sannan a matayinmu na dattawa, kuma a ce an sa mana shugaba wanda ba dattijo ba''?, a cewarsa.

Ya ce kamata ya yi a bar mambobin majalisar da kansu, su zaɓi wanda suke ganin ya cancanta.

Kujerun shugaban majalisar dattawa da ta kakakin majalisar wakilan Najeriya na da matuƙar muhimmanci da tasiri a siyasar Najeriya.

BBC

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki