Alhassan Doguwa ya yi tazarce a karo na hudu

 


Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa ya ci zabe a karo na biyar.

Baturen zaben da aka kammala a ranar Asabar, Farfesa Sani Ibrahim, ya ce Alhassan Ado Doguwa ya yi nasarar komawa kan kujerarsa ne bayan ya samu kuri'u 41,573 a yayin da dan takarar jam'iyyar NNPP, Yusha'u Salisu, ya zo na biyu da kuri'u 34,831.


Idan za a iya tunawa bayan zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Maris, INEC ta bayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara.


Amma daga bisani aka janye nasarar Doguwa bayan da baturen zaben, Farfesa Ibrahim Yakasai ya cewa tursasa masa bayyana sakamakon aka yi, don haka bai samu nutsuwar yin lissafin kuri'un da aka jefa yadda ya kamata ba, kasancewar rayuwarsa da ta ma'aikata na cikin hadari a lokacin.


Amma daga baya da aka yi lissafi aka gano zaben bai kammalu ba saboda kuri'un da aka soke sun zarce tazarar da ke tsakanin kuri'un Doguwar da na Yusha'u.


Hakan ne ya sa aka kammala zaben a yau, wanda Alhassan Ado Doguwa ya yi nasara.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki